HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 36

HAƊIN ALLAH: Labarin Soyayya Mai Rikitarwa, Fita Ta 36

HAƊIN ALLAH

   Labari da rubutawa
       
   *Hauwa'u Salisu (Haupha)* 

       Page 36

Barista Alawiyya ta nufi inda shugaban tsafin yake cike da ɓacin rai, domin a hasashenta yanzu lokacin tashi daga kotu ma ya wuce, tabbas an zauna Mamarta bata da mai kare ta, tabbas wannan ma wata ɓaraka ce mai girma da ke iya jefa mahaifiyarta a taskun karaya da shari'ar, koma ta ɗauka wani mummunan abu ne ya faru da ita ba wanda ya sani, ga shi kuma ba wanda tai waya da shi a cikin Daddy ta mijinta .

Cike da ƙwarewa a harkar tsafi ya nuna ta da yatsansa, wani farin hayaƙi ya fito ya nufe ta, sai dai abin mamaki kafin ya isa inda take ya ɓace ɓat.

Cikin azama ta fizgo shi ta watsar ƙasa kafin ya ankara ta sa hannu ta naushe mai hanci da baki take ya suma jini ya ɓalle ta  baka ta hanci.

Cikin sauri ta bubbuɗe duk sauran ɗakunan sai ga yaran ta gani kwance suna barci wanda ba mamaki na sirihi ne. Da azama ta ɗauke su duka duk da sun mata nauyi haka ta daure ta nufi ƙofar barin falon baki ɗaya sai ta tuna da sauran mutanen da ta gani a ɗakunan don haka ta leƙa ta daka masu tsawa tace su biyo ta, nan take suka fito wasu kuma sun kasa tashi tace ma masu dama-damar su taimaka masu kafin su fice waje.

Suna fita yaranta da har sun fara tunanin ko rana ta ɓaci ne suka taso da hanzari suka amshi yaran suka saka a mota, nan ne suka gaya ma mutanen su jami'an tsaro ne, sannan suka kwantar da hankalinsu har ma wasu suka fara zubewa alamar sun gaji.

Daidai lokacin kiran Daddy ya shigo wayarta, cike da fargaba ta ɗaga kiran, don jin me ya samu Mamarta.

"Yarinyar kirki ina so nai maki albishir mai matuƙar saka farin ciki."

Sai yanzu hankalinta ya kwanta, "Daddy Ina jinka me ya faru a kotun ne?"

"Barista Jiddah ce ta bayyana kamar yadda guguwa ke bayyana gaban kafirai tai ma shari'ar ɗibar karan mahaukata, abin gwanin mamaki yadda aka ce sun saye Alƙalin amma sai ga shi zuwanta ya kasa aiwatar masu da ƙudurinsu."

Cike da matuƙar farin ciki take cewa, "Daddy kana nufin Jiddah tawa Jiddah ta Iyami ce ta bayyana a kotun matsayin Baristar Mama?"

"Ko shakka babu a wannan maganar Ɗiyata." Cewar Daddy cikin farin ciki da walwala.

"Daddy ga ni nan zuwa yanzu nan nima na gano yaran na amso su kuma yanzu haka ina tare da su a mota."

"Yawwa ɗiyar albarka, sai dai ban samu damar magana da ita, ta ɓace min, amma na ganta tare da wani mutum ba mamaki mijinta ne, sannan an ɗage zaman sai nan da sati guda."

"Shike nan Daddy, yanzu zan zo ina fatan kuna gida a waje guda ba kuma wata matsalar?" 

"Tabbas kuwa ba wata matsala sai dai fa ina ga sun rufe ma Fatima baki domin ta kasa furta ko da kalma guda daga bakinta duk tambayar da ake mata hawaye kawai ke zubowa, kuma tabbas naga son yin magana daga bakinta." 

"Shike nan Daddy akwai Allah ai, kuma yanzu haka na gama da gidan tsafin nasu don ƙona shi zan duk da Dodon tsafin nasu."

Haka kuwa akai Barista Alawiyya ta ba yaranta umarnin sa ma gidan wuta, nan take kuwa suka saka ma gidan wuta baki ɗaya. Sai ga kukan Dodon sun ji yana ta ihu yana gurnani har ya halaka gidan ya koma kango sannan Barista Alawiyya ta ja motar yaranta na biye da ita da sauran mutanen da suka fito daga cikin gidan suka nufi gari .

Oga Dauda kuwa bai san lokacin da imanin dole ya shige shi ba. Tabbas duk wanda ya haɗa hannu da Barista Alawiyya sai ta karya mai hannu, kowa ya ci tuwo da ita ya amince da miya kawai ya sha, domin shi jiyau ne kuma ganau ne kan lamarin Barista Alawiyya Bello Gareji.

Tun da Barista Jiddah ta shigo cikin ɗakin shari'ar idonsa ya sauka a kanta, tun da ya auri matarsa Alawiyya bai sake tunanin zai iya kallon wata mace da fuskar soyayya ba, domin ita kawai yake gani ya ga komai nata ya yi mai. Ita kawai ce ke saka shi nishaɗi ko da bata ce mai komai ba, haka kawai idan ya tasa ta gaba yana kallo sai ya ji yafi kowa farin ciki, amma Yau yana ɗora idonsa kan Jiddah ƙawar matarsa Alawiyya sai ya ji duk duniya babu wadda take so irinta, ba wai don ya daina son matarsa ba, a'a sai dai kawai ita nasa son daban ne kamar yadda na Jiddah yake daban a cikin zuciyarsa daga ganinta yanzu.
Yasan akwai matsananciyar damuwa a lamarin sai dai ba shi ne ya ɗora ma kansa ba, daga kallo guda ya samu kanshi da ƙaunar lol llta wanda ko tantama bai yi hakan ake kira da "HAƊIN ALLAH" saboda haka dole Alawiyya tai haƙuri ta barshi ya auri ƙawarta Jiddah, ko da yake idan har da gaske take tana son Jiddah ta kuma ɗauke ta matsayin da take ta ambata to ita ce mace ta farko da zata fara ba shi shawarar auren Jiddah.

Hakan yasa ko za a tambaye shi abin da ake cewa gun da yadda akai gun ba zai iya maimaita wa ba, saboda shi ya tafi duniyar tunanin yadda zai auri Jiddah.

A matsayinsa na likita akwai alamomin da yake gani nan take yake gane matar aure da budurwa har ma da wadda ta taɓa aure, bazawara, to tabbas ya ga cewar Jiddah bazawara ce don haka ba zai bari wani ya shiga tsakaninsa da ita ba.


      Jiddah kuwa suna dawowa daga gidansu Hajiya Turai ta shige sashenta bayan ta nuna ma Mustapha na shi sashen kamar yadda mai gabatarwa ya gabatar mata da hakan.

Tana shiga ta watsa ruwa ta jawo wayarta ta gwada kiran lambar Alawiyya da ta ɗauka gun Lauyar data taimaka mata da aron kayanta ta saka na aiki mai suna Barista Asiya Sada.

Tana kira ta shiga amma har ta katse bata ɗaga kiran ba, hakan yasa hankalinta ya tashi sosai har ta tashi zaune ta sake kiran lambar.

Daidai lokacin Alawiyya na toilet sai Dr Falsal dake zaune abin duniya ya dame shi na tunanin Jiddah. Ganin an dame shi da kiran yasa ya ɗaga kiran da zummar cewa bata kusa domin layin wajen aikinta ne  ake kira.

Ita kuma Jiddah jin an ɗaga kiran yasa ta fasa ihu tana kiran sunan Alawiyya yasa Dr Falsal ɗaukewar numfashi na gudun sa'a guda tsabar jin zaƙin muryarta da ya yi duk da a cikin matuƙar ihun murna take maganar. Cewa take.
"Don Allah da gaske da Alawiyya nake magana? Don Allah ke ce Alawiyya ta wadda nake nema shekara da shekaru? Don Allah da gaske daman kina nan Alawiyya?"

Cike da sanyin murya ya ce, "Mijinta ne tana wanka ita, amma zan faɗa mata kin kira idan ta fito."

Jim tai, amma sai ta samu kanta da gaida shi cikin jin kunyar yadda ta cika mai kunnuwa da hayagaga.

Ya amsa yana jin tamkar kar da ta dakata da maganar saboda yadda yake jin muryarta tamkar busar sarewa.

Jiddah jin ya yi shiru tana ta magana yasa ta ɗauka network ne ya samu matsala don haka ta kashe wayar tana jin daɗin ta ji muryar mijin Alawiyya alamar da gaske zata haɗu da Alawiyya.

Tuno hakan yasa ta miƙe ta fara shiri don tasan Alawiyya na fitowa kiran da zatai mata shi ne tana ina? Ita za ta zo ko ita ta je, to amma gwara ita ta je saboda ita ba miji gareta ba, don haka bai kamata ta fito da Alawiyya daga gidanta ba,bayan mijinta na gida ba.

Tana gama shiryawa ta kira Mustapha a waya tace ya shirya za su je gidan Alawiyya, sai kawai ya samu kanshi da jin faɗuwar gaba sosai jin ta ambaci gidan Alawiyya. Amma ba yanda zai yasan wacece Alawiyya gun Jiddar don haka ya kimtsa ya fito falo yana jiranta.

Tana fitowa ji ya yi kamar ya ce ta koma ta sauya kaya, ganin yadda tai matuƙar kyau kamar ka ɗauke ta ka ruga. Bai taɓa ganin mace mai kyau da kyan jiki irin Jiddah ba,komai nata ya yi mata cif kyakkyawa ajin farko ajin ƙarshe gun kyau, ga baiwar fara'a Allah ya bata.

Ganin yana ta kallonta ya kasa magana sai kunya ta kama ta, kawai sai ta ga rashin dacewar zuwa gidan Alawiyya da gyale bayan tasan mijinta na gidan, don haka sai ta koma ta sako hijabi babba ta fito.

Ko da ya ganta cikin hijabin sai ya ga tafi kyau fiye da gyalan ma, hakan yasa ya amince da cewar komai Jiddah zata saka sai ya yi mata kyau. 

Zata kira lambar kenan kiran Alawiyyar ya shigo a wayarta, cike da ɗoki ta ɗaga kiran tana cewa, "Kawai ki turomin da adireshin ga Ni nan a kan hanya."

Cike da ɗoki ita ma Alawiyya ta kashe wayar ta kasa furta ko da kalma guda jin muryar Jiddah, sai kawai ta kashe wayar ta fashe da kukan murna tana tura mata kwatancen gidan da suke.

Da sauri Dr Falsal ya shige wanka jin zuwan Jiddah, nan da nan ya fito ya saka kaya masu kyau ya zuba turare ya dawo falo yana jiran ta inda zai fara hasko fuskar Jiddah a idanunsa cikin gidansa.

Da sauri Alawiyya ta kimtsa tai abinci mai sauƙi ita ma ta zuba kwalliya ta zauna jiran zuwan Jiddah.

To masu karatu ko ya haɗuwar zata kaya? Shin Dr Falsal zai gayama Jiddah burinsa ne ko Alawiyya zai gaya mawa?

Ku dai ku biyo Haupha don jin yadda zata kasance.

Taku a kullum Haupha ✍️