DA AURE NAH: Labarin Yaudara Mai Muni, Fita Ta Farko

DA AURE NAH
NA HAUWA'U SALISU (Haupha)
Bissimillahirrahmanirrahim! Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallam.
Page 1
Tsaye suke kan kwanar layin, ya zuba mata ido yana bin ta da wani mayetaccen kallo, ita kuma ta sadda kanta ƙasa.
Dan haka nace ya kamata na jiyo meke faruwa a can?
"Ina son ki ɗago kanki ki kalleni, sannan ki sa idanunki a idanuwana Huwailat,don na tabbatar da gaskiyar abin da bakinki ya faɗa.
Ni dai nasan Allah shi ya ɗora min sonki da ƙaunarki a zuciyata don haka ban jin akwai wani abu da zai kauda ƙaunarki a zuciyata.
Huwailat ki san yadda zafin ƙauna take a zuciya kuwa? Tabbas nasan baki sani ba da kin sani ba abin da zai sa ki dinga wasa da numfashina."
Ta ɗago ta kalleshi so ɗaya ta sadda kanta ƙasa tana murmushi tana jin daɗin kalaman da Yusuf ke fada mata duk sadda suka haɗu, ji take tamkar tafi kowa sa'ar masoyi a duniya.
"Magana nake dake fa Huwailat amma kin ƙi magana, kin san da cewa maganarki na bani ƙwarin gwiwa sosai wajen ganin mun cika muradinmu."
Ta sake ɗago kai ta kalle shi fuskarta ɗauke da murmushi ta ce, "Ban san abin da zance ma ba, amma nasan dai kai ne farin cikin raina, sannan kaine cikar muradina ina farin ciki naga ranar da burinmu zai cika...
Tana ɗaga ido ta hango wani dake tafowa naga tai maza tabar gun,kamar haɗin baki shima Yusuf yai nasa hanyar.
Abun tambaya waye wanda ya katse ma masoyan nan hanzari? Ku biyo Haupha don jin cikakken labari mai cike da ban tausayi ban takaici cin amana kai har da yaudara!
♦♦♦♦♦♦