Yadda Cire Tallafi Zai Kare Lafiyar 'Yan Najeriya---Kashim Shattima

Yadda Cire Tallafi Zai Kare Lafiyar 'Yan Najeriya---Kashim Shattima


Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana amfanin cire tallafi ga lafiyar 'yan Najeriya. Ya ce cire tallafin zai kare mutane daga shakar gurbatacciyar iska da ta kai Tan miliyan 15 a shekara daya. 
Shettima ya bayyana haka ne a taron karawa juna sani da Hukumar Sauyin Yanayi ta Kasa (NCCC) ta gudanar a Abuja, New Telegraph ta tattaro. 
"A farkon wannan gwamnatin, Shugaba Tinubu ya yi ta maza ya cire tallafin man fetur a kasar. " A binciken da hukumar sauyin yanayi ta kasa ta fitar kan amfanin cire tallafin man fetur ya nuna an samu raguwar siyan man da kashi 30. 
Hakan ya kawo raguwar shakar gurbatacciyar iska da mutane ke shaka a kullum har Tan 42,800. Ya ce hakan bai rasa nasaba da rashin yawan ababan hawa a kan tituna ya assasa saboda raguwar hada-hada a kan hanyoyi.