Malami Gebawa dake kauyen Durbawa a karamar hukumar Kware ta jihar Sakkwato an zargi ya karya kafa da hannun daman matarsa saboda ta je asibiti ba da izininsa ba.
Da take bayanin yadda lamarin ya faru Malama Halimatu Sadiya wadda take kwance a asibitin kashi dake garin Wamakko ta ce mijinta ya karya mata kafa da hannu ne saboda ya ga magani a banta bayan ta dawo duban mahaifiyarta da ba ta da lafiya.
"Kusan wata hudu a yanzu ina fama da rashin lafiya, ya sani(mijinta) har ma'aikacin kiyon lafiya ya kira ya sanya min ruwa amma ciwon sai karuwa yake yi.
"Na roke shi ya barni na je asibiti a duba ni amma bai aminta ba, har wani dan uwana ya so ya kai ni asibiti da kudinsa amma mijina ya ki yarda.
"A lokacin da na je duba mahaifiyata da ba ta da lafiya, anan ne na tambayi shawara ga ma'aikacin lafiyar da yake dubata, sai ya bani wasu magunguna na yi amfani da su.
"Bayan na dawo gida ne ya ga maganin daga nan ya fara fada, na tafi asibiti ba da izininsa ba, na fada masa ba haka ba ne wanda yake duba mamata ne ya bani su.
"Ya nuna shi ba zai aminta ba sai na kai shi wurin wanda ya ba da maganin, na yarda zan kai shi, a lokacin da nake sanya tufafi na a dakina ya shigo sai ya rufe kofa ya fara dukana da sanda sai da takare
"A lokacin da ya fahimci ya kare min kafa da hannu sai ya dakata ya fara kuka yana rokona kar na fadawa kowa abin da ya faru tsakaninmu ko da wani ya tambaye ni na ce dan acaba ne ya kayar da ni a babur.
Mijin Malami ya aminta da laifinsa ya ce sharrin shedan ne, amma dai matarsa ta je asibiti ba da izininsa ba duk da kokarin da yake yi mata da danginta duk sanda ba su da lafiya.
"Bayan ta dawo wurin dubin mahaifiyarta da ba ta da lafiya, na ga wani kulli a cikin bokiti da ta zo da shi na so nasan ko mine ne amma ta ki barin na sani.
"Na matsa sai nasan ko mine ne, na kwace bokitin a lokacin da take son ta gudu da shi, dana bincika sai na ga katin asibiti da da magani da butar karfe.
"Sai na tambaye ta ya zaki tafi asibiti baki sanar da ni ba, tun da ta san a koyaushe ina kula da rashin lafiyarta a satin da ya gabata sai da na kawo mata ma'aikacin kiyon lafiya ya duba ta,"a cewarsa.
Malami ya karya ta cewa ya bugi matarsa da sanda ya ce a lokacin da take son sai ta karbi bokiti a hunnunsa ne ta fadi ta samu rauni a hannu da kafarta.
"Bayan ta samu matsala a kafa da hannu na kira mai dori ya gyara, dan uwanta ya kira wani ya gyara sai da na biya dubu 50, dan uwanta ya kawo wani shima sai da na biya dubu 25 na magani.
"Ni ne shugaban kungiyar banga na yankinmu kuma ni manomi ni dan karamin abin da nake da shi nake kula da ita tare da macen da ke jinyarta," a cewarsa.
Malami ya yi da ya sanin abin da ya faru "na yi sanadin samun rauninta don haka na dauki kaddarar abin da hakan zai haifar.
"Amma don Allah matata kar ki barni don ina sonta, ina son ki sosai nima nasan tana so na, ku ba ta hankuri kar tabarni," ya roka.
Mi ya sa baku barin iyalanku na zuwa asibiti, ya ce "saboda ba wata asibiti mai aiki a yankinmu."
Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jiha ASP Ahmad Rufa'i ya ce har yanzu maganar ba ta kawo saman teburinsa ba.
Sai dai ana rade-raden an kama mijin an mika shi ga hukumar 'yan sandan Sakkwato.