Akalla mutum 19 ne masu sana'ar kayan Tireda 'yan bindiga suka kashe a kasuwar Unguwar Lalle cikin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato a jiya Jumu'a.
Maharan sun yiwa mutane da dama rauni mafiyawansu na karbar magani a babbar asibitin Sabon Birni.
Manema labarai ba su tabbatar ko wannan harin ramuwa ce kan abin da 'yan banga suka yi na kashe mutane 11 a kasuwar Mammande a ranar Alhamis data gabata ba.
Garin Unguwar Lalle yana kan hanyar Goronyo zuwa Sabon Birni suna fama da aiyukkan mahara a watannin nan.
Akwai wasu sojoji biyar da ke aikin bayar da tsaro a yankin 'yan bindiga suka yi masu kwantan bauna suka kashe su a watannin da suka gabata.
Wani mazauni garin ya shedawa jaridar Daily Trust cewa harin ya faru a lokacin da ake cin kasuwa.
Unguwar Lalle kasuwarsu tana cikin manyan kasuwannin da ake ci a yankin na gabascin Sakkwato da yawan 'yan kasuwa a Sakkwato da Kebbi da Zamfara da makwabciyar Nijeriya waton Nijar ke zuwa cin kasuwar.
Har yanzu ba a kididdige wadanda suka rasu ba amma akwai majiyar da ta ce akwai wasu 'yan uwan juna biyu da ke sana'ar fata da aka kashe.
Majiyar ta ce yaya ne da kanensa da suke uwa daya sun tafi kasuwar ne daga cikin gari haka ta faru da su, har an yi masu Janaza a rufe su a makabartar Tudun Wada a Sakkwato.
'Yan bindigar sun mamaye kasuwar ne bayan an dawo masallacin jumu'a sun zo ne wuraren karfe uku na rana suka rika harbi kan mai uwa da wabi, bayan nan an ga gawar mutum 19 in da ba a san in da sauran mutane suke ba.
Dan Majalisa mai wakiltar Sabon Birni ta Arewa Aminu Almustapha Gobir ya ce gaba daya Sabon Birni tana fama da hare-haren 'yan bindiga, maharan sun mamaye ta.
Gobir ya halarci janazar 'yan kasuwar da suke 'yan uwan juna da aka kashe, ya fahimci 'yan kasuwar da aka kashe sun zo ne daga bangarori daban-daban.
Gwamnatin jiha ta ga laifin 'yan kasuwar kan kin bin umarnin gwamnati da ta hana cin kasuwa a yankin amma suka yi gaban kansu.