CHICKEN SANDWICH:Haɗin Kaza Na Musamman Don Lokaci Na Musamman

CHICKEN SANDWICH:Haɗin Kaza Na Musamman Don Lokaci Na Musamman

BASAKKWACE'Z KITCHEN


CHICKEN SANDWICH:
 


 
INGREDIENTS
slice bread,
kaza
albasa
attarugu
tafarnuwa(optional)
curry
salad
gishiri
maggi.


 
METHOD
Dafarko uwar gida ki dafa kazarki da kayan qamshi sai ki cire fatar jikin da qashi, sai ki yanka siri siri,
*sai ki yanka albasa circle,ki daka attarugunki da tafarnuwa kadan, sai ki dan diga mai a kasko ki zuba albasan a kai kina juyawa har tayi laushi, amma kada ya soyu yayi baki, sai ki zuba attarugu da tafarnuwa, ki ci gaba
da soyawa,
 sai ki kawo yankakken naman kazar ki zuba a kai ki sa maggi da curry yanda tst in ya miki, su soyu kamar na 5-6minute, sai ki sauke, sannan ki zuba salad cream da waken gwangwani idan kina so ki cakuɗa
ki Ringa zubawa a cikin bread yanka ɗaya kina rufewa da wani yanka ɗayan sai ki
gasa shi. ƴar uwa zaki iya tashi da safe kiyi wa mai gida breakfast dashi....

 
MRSBASAKKWACE