Burinmu mu sauya masu ƙarancin tunanin Ƙwaƙwalwa daga shugabancin Nigeriya-- We2geda
Daga Ibrahim Hamisu.
Ƙungiyar matasa domin sabunta shugabancin ƙasar nan wato We2geda ta ce tsofaffi masu karancin tunanin ƙwaƙwalwa ne suke kankane komai, kuma suka daurewa sarasuka gindi, wanda ya ce ba za su lamunce da hakan ba,
Shugaban ƙungiyar kuma wanda ya Assasa tafiyar Alh. Ibrahim Hussain Abdulkarim ya bayyana haka yayin taron ƙaddamar da shugabancin ƙungiyar a shiyar kudu
maso kudancin Nigeriya, da ya gudana a birnin Oyo ta jihar Akwa-ibom a karshen makon jiya,
Ibrahim Husain ya kara da cewa " Tun 1990 ake walagigi da mu sai a kadamu can sai a kadamu can mun gaji, amma manufar We2geda shi ne mu zo mu dunƙule guri guda babu banbancin jam'iyya, mu ayiye duka jam'iyun mu, mu ajiye ubannin gidanmu, mu zauna mu kalli ƙasar ita kanta mu kalli yanyanmu da jikokinmu mu tsaya mu yi wa kasarmu aiki,
"Don haka muke cewa tunda wadannan dattawan sun kasa hada kansu, zaben fidda gwani ma sun kasa, saboda ba su dauki matasa da muhimmanci ba, kuma ba za su iya tunani da tunaninmu ba, don haka mun yadda kowane dattijo yana da ta sa hikimar, mu kuma muna da kazarkazar idan aka hada sai ka ga mun kai kasarmu inda ake bukata" a cewar Alhaji Ibrahim Husaini
Kungiyar We2geda dai tun bayan ƙaddamar da i ta da aka yi a Kano, ta kuma ƙaddamar da shugabancin Ƙungiyar a Jahohin Legas, Adamawa da kuma Akwa-ibom.
managarciya