'Yan sandan Legas sun kama Motoci makare da Alburusai a hanyar su ta zuwa Katsina
.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas, ta cafke wasu motocin bas guda biyu makil da manyan katosai masu rai, tarwatsa babura guda uku a Estate Poromope, kan titin Ijede, Ikorodu, jihar Legas.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya sanyawa hannu a ranar Asabar, jami’an sashen na Ikorodu sun kama wasu.
Hundeyin ya ce, “Bincike na farko ya nuna cewa wadanda ake zargin, Tukur Abdullah mai shekaru 35, Muazu Telim mai shekaru 50 da Dahiru Idris mai shekaru 36 suna kan hanyarsu ta zuwa jihar Katsina.
“Wadanda ake zargin, da kayayyakin baje koli da kuma motocin, masu lambar rajista KMC 438 YK da KMC 394 XF an mika su hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Ikeja domin ci gaba da bincike.
managarciya