Rigimar PDP: Atiku da Gwamnonin PDP Sun Gana  a Abuja

Rigimar PDP: Atiku da Gwamnonin PDP Sun Gana  a Abuja

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023, Alhaji Atiku Abubakar, na ganawar sirri da gwamnonin PDP yanzu haka a Abuja. 

Abokin takarar Atiku a zaben da ya gabata kuma tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, na cikin mahalarta taron wanda ke gudana a Anguwar Asokoro. 
Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasa na tsawon zango biyu, ya tabbatar da haka a wani rubutu mai haɗe da Hotuna da ya wallafa a shafinsa na facebook. 
Wannan taro na masu ruwa da tsakin PDP ba zai rasa nasaba da yanayin yadda harkokin babbar jam'iyyar adawa ke tafiya a yanzu ba, rigingimun cikin gida sun baibaye ta. 
Ana tsammanin taron zai tattauna kan yadda za a sake fasalin jam'iyyar PDP ta yadda zata farfaɗo bayan kashin da ta sha a babban zaɓen 2023 da ya gabata. 
Duk da ana tsammanin dukkan gwamnonin jam'iyyar PDP zasu halarci taron na masu ruwa da tsaki, zuwa yanzu da muke haɗa wannan rahoton gwamnoni 7 ne suka isa wurin.