Gwamna Sokoto Ya Yi Watsi da Batun Zanga Zanga, Ya Fadi Matakan da Ya Dauka

Gwamna Sokoto Ya Yi Watsi da Batun Zanga Zanga, Ya Fadi Matakan da Ya Dauka

 
Gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ta ƙudiri aniyar ƙin shiga zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a faɗin ƙasar Nijeriya. 
An ɗauki matakin ne a zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki wanda ya samu halartar shugabannin ƙungiyoyin siyasa dana addini dana ɗalibai da kuma shugabannin ƙwadago. 
An gudanar da zaman ne a ranar Juma'a, 26 ga watan Yulin 2024, don fadakar da jama'a.
Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana matsayarsu, inda ya ce mahalarta taron sun yanke shawarar kada su shiga zanga-zangar saboda “ba ta da amfani”. 
Gwamnan ya nuna damuwarsa kan halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan na taɓarɓarewar tattalin arziƙi, hauhawar farashin kayayyaki, da rashin tsaro.
Ya bayyana wasu daga cikin matakan da gwamnatinsa ta ɓullo da su domin taimakawa wajen rage raɗaɗin wahalhalu da suka haɗa da, biyan albashi duk wata a ranar 19 ga wata. 
Sauran su ne raba kayan abinci, rabon takin zamani, bayar da kyautar kuɗi a lokutan bukukuwa da dai sauransu. Gwamnatin jihar ta kuma jaddada ƙudirinta na yin hadin gwiwa da dukkanim bangarorin da abin ya shafa domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.