Baya ba zane: MDD ta buƙaci a tsagaita wuta a Gaza domin a yi wa yara rigakafin Polio
Hukumomi a Majalisar Ɗinkin Duniya sun buƙaci a tsagaita wuta na kwana biyu zuwa bakwai a Gaza domin a bayar da damar yi wa yara fiye da dubu 640 allurar rigakafin cutar polio.
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya ce suna shirin fara rigakafin nan da ƙarshen watan Augusta.
A watan daya gabata ne aka gano ƙwayar cutar a tarkacen shara a wasu yankunan Gaza biyu.
Kiran Majalisar Ɗinkin Duniyar ya zo ne a yayin da za a shiga kwana na biyu don ci gaba da tattaunawar da ake a Qatar a kan batun tsagaita wuta da kuma sakin waɗanda aka yi garkuwa da su.
A Gaza kanta, rundunar sojin Isra'ila ta sanar da umarnin kwashe Falasɗinawa a wasu larduna biyu.
Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa Isra'ila za ta matsalar da sansanonin da ta samar na tudun mun tsira saboda bayanan sirrin da ta samu a kan cewa Hamas ta samar da mafaka a wajen.
managarciya