Kungiyar Rayuwar Mata ta Nijar ta Rabawa Iyalai  200 Tallafin Abinci a Maradi

Kungiyar Rayuwar Mata ta Nijar ta Rabawa Iyalai  200 Tallafin Abinci a Maradi

Daga Mukhtar A. Halliru Tambuwal, Sokoto.


Ƙungiyar Inganta Rayuwar Mata Musulmi ta Association Islamique Rayuwar Mata ( A.I.R.M)  da ke tallafawa mata zawarawa da marayu da mabuƙata a Jamhuriyyar Nijar ta raba abinci ga mutane 200 da aka zaƙulo daga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a kwanakin baya. 

An ƙaddamar da rabon abincin ne a makarantar Raudatul  Ibadurrahmane da ke garin Maraɗi, a Jamhuriyar Nijar ƙarƙashin jagorancin shugabar Ƙungiyar Malama Khadejar Abubacar. 

Shugabar ta bayyana cewa, "Wannan tallafi an samo shi ne da haɗin gwiwar wata baiwar Allah da ke zama a Dubai ta hannun wani shiri na kungiyar 'Big Up Project' da ke ƙarƙashin Shugabar Ƙungiyar Melani." 

Shugabar ta ƙara da cewa, an raba shinkafa kilo 25, man girki lita 2, katon ɗin taliya da zanin rufa, kasancewar an shiga lokacin sanyi. 

Yayin da shugabar take yabawa waccea ta bada gudunmawar ta yi kira ga waɗanda suka amfana da su yi amfani da shi yadda ya dace. Sannan ta buƙaci Gwamnati da ta ƙara ƙarfafawa matasa gwiwa ta hanyar koya masu ƙananan sana'o'i don su samu abin dogaro ga kansu ba sai sun jira an ba su ba. 

Ta yi godiya ga Gwamnan Maraɗi bisa goyon bayan da yake ba su a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso. 

Gwamnan Jihar Maraɗi, Babban Kwantirolan 'Yansanda Issoufou Mamman, ya yabawa ƙungiyar bisa goyon bayan da take bai wa Gwamnati, sakamakon kiran da take yi kan kowa ya yi nasa ƙoƙarin wajen taimakawa al'umma, a maimakon barin Gwamnati kaɗai ga aikin jinƙan al'umma.

Wasu da suka amfana sun yi godiya ga wadda ta taimaka da kuma ƙungiyar Rayuwar  Mata, da ta yi wannan ƙoƙarin. Sun bada tabbacin yin amfani da abin da aka raba musu yadda ya dace, tare da kira ga masu hali da suka ƙara taimakawa kasancewar akwai mabuƙata a cikin  al'umma da yawa. 

Taron ya samu halartar mambobin ƙungiyar da sauran al'ummar Maraɗi daga ɓangarori daban-daban. 

Ita dai wannan ƙungiya na ƙoƙarin ganin an tallafawa al'umma musamman mabuƙata, inda take faɗi tashin ganin an samo masu ɗauki daga ciki da wajen ƙasar.