Gwamna a Arewa Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashin N70,000 

Gwamna a Arewa Ya Yi Amai Ya Lashe Kan Fara Biyan Ma'aikata Sabon Albashin N70,000 

Gwamna Abdullahi Sule ya ce jihar Nasarawa ba ta da ƙarfin tattalin arzikin da za ta biya ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000. Gwamna Sule ya ce ko da jihar za ta iya aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 sai nan da shekaru biyu masu zuwa. 
Abdullahi Sule ya bayyana haka a wurin ganawarsa da wakilan ƙungiyar kwadago wanda ya gudanaa a gidan gwamnati da ke Lafia. 
Kamar yadda Vanguard ta tattaro, taron ya maida hankali ne kan yadda za a inganta walwalar ma'aikatan gwamnati a jihar Nasarawa. 
Wannan kalamai da gwamnan ya ci karo da wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Peter Ahemba ya fitar cewa Nasarawa da dab da fara biyan albaahin N70,000.
Gwamnan ya shaidawa ƴan kwadagon cewa gwamnatinsa za ta yi ƙoƙarin karawa ma'aikata girma wanda ba a yi ba a tsakanin 2019 zuwa 2023. 
"Ban manta da cewa fiye da watanni biyu da suka gabata mun amince za mu yiwa ma'aikata karin girma na tsakanin 2019 zuwa yau, wato daga 2019-2023.
"Ba za mu bari mu koma gidan jiya ba, irin wannan matsala da na gada, inda na taras da sama da shekaru takwas ba a yi wa ma’aikata karin girma ba.” 
Gwamna Sule ya amince da yiwa ma'aikata karin girma bayan da ƴan kwadago sun bukaci a dakatar da aiwatar da sabon mafi karancin albashi na wani dan lokaci.
"A wancan lokaci na faɗa maku mu jira muka yadda za ta kaya game da ƙarin albashin.
Yanzu mu ɗauko ya zo mana da ƙarin N800m, idan muka haɗa da N200 da muke biya ya zama N1bn.
"Kun ga jihar mu ba za ta iya biya ba, ba mu karfin tattalin arzikin da zamu iya biyan wannan adadi duk wata," in ji Sule. 
Kuna da labarin Bayan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da N70,000 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata, ana bukatar gwamnoni su fara aiwatarwa Kungiyar manyan ma'aikatan kasar nan (ASCSN) ta yi barazanar daukar mataki a kan gwamnatocin jihohi da su ka ki fara aiwatar da sabon albashin.