Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar Da Shirin Karin Kudin Data Dana Kiran Waya—Shaikh Pantami
Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin karin harajin da ta ke shirin yi kan ayyukan sadarwa. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ministan Sadarwa da bunkasa Tattalin Arziki ta hanyar fasahar zamani Isa Pantami ne ya sanar da hakan a yayin taron kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan kudaden harajin.
Shirin dai an gudanar da shi ne a Babban Birnin Tarayya Abuja ranar Litinin.
Pantami ya ce, Gwamnatin Tarayya ta yi fatali da aiwatar da harajin, wanda ya bayyana a matsayin nauyi ga bangaren sadarwa.
Ya kuma kara da cewa, ba a tuntubi ‘yan majalisar dokokin kasar nan ba, kafin yanke hukuncin karin harajin.
Kazlaika Pantami ya ce shi da kan sa ya yi watsi da wannan manufa, ya kuma shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi watsi da ita duba da irin illar da za ta yi ga tattalin arzikin fasahar zamani.
A cewarsa, bullo da harajin ga Kamfanonin sadarwa da fasahar sadarwa zai kawo cikas ga nasarorin da aka samu a baya.
Sai dai tun da fari ministar kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed ta zarge shi da yin zagon kasa ga kokarin gwamnati na tabbatar da wannan karin harajin.
managarciya