Ambaliyar Ruwa: Dan Majalisar Wakilai Ya Ziyarci Al'ummar Mazabarsa a Yobe

Ambaliyar Ruwa: Dan Majalisar Wakilai Ya Ziyarci Al'ummar Mazabarsa a Yobe

 

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

 

A wata ziyarar jaje da ya kai a mazabarsa; Hon. Zakari Ya'u Galadima, Dan Majalisar Wakilai, mai wakiltar kananan hukumomin Bade da Jakusko a jihar Yobe, domin jajanta wa jama'a, sakamakon ibtila'in ambaliyar ruwa da ya mamaye garuruwa; inda ya rusa daruruwan gidaje tare da lalata amfanin gonakin jama'a a kananan hukumomin, da wasu sassan jihar, al'amarin da ya jefa dubban jama'a cikin mawuyacin hali. 

 
Dan majalisar, Zakari Ya’u Galadima wanda tawagarsa, a ranar Laraba ya fara da yada zango a Fadar Sarkin Bade; Alhaji Mai Abubakar Umar Suleiman, ya koka tare da bayyana alhininsa dangane da yadda mazabar sa ta yi babbar asara sakamakon wannan ambaliyar ruwa.
 
Ya ce, “Kamar yadda kuka sani, wannan ibtila’in ambaliyar ruwa da ya afku a fadin kasar nan, a wannan shekara, kuma al'amari ne maras dadi ta la'akari da asarar da ya jawo a mazabata; kuma duk da yake yankin Sahara ne, amma bai tsira ba daga ambaliyar ruwan. Wanda zan iya cewa ambaliyar ruwa ta shafi ko’ina a mazabar Bade/Jakusko tare da lalata gidaje da amfanin gonakin jama'a.”
 
A cewarsa, duk da karancin tallafin da ya bayar ga wadanda ibtila'in ya shafa, wanda suka hada da kayan abinci, fatun buhunan leda domin tare ruwan, ya ce, “Mun yi kokari wajen kai koken jama'ar wannan mazaba inda ya dace a gwamnatin Tarayya da makamantan hakan, domin daukar matakan gaggawa wajen tallafa wa al'ummar. Sannan kuma mun ziyarci masu ruwa da tsakin a wannan mazaba tamu don jajantawa."
 
"Mu na yi jama'a jaje da addu'ar Allah ya saukaka mana tare da mayar mana da fiye da abin da muka yi asarar sa ta dalilin wannan ibtila'in ambaliyar ruwan." In ji Ya'u Galadima. 
 
Galadima ya ci gaba da bayyana cewa, "A matakin gwamnatin tarayya mun gudanar da tarurruka da dama da wasu 'yan majalisar jihar ciki har da shugaban majalisar dattawa, wanda daga bisani mun mika sakamakon taron ga hukumomin bayar da agajin gaggawa don tallafa wa jama'ar mu."