Zamu Tabbatar Da Jindadi Da Walwalar Matasa----Honarabul Kabir Tukura

Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya tana sane, da irin muhimmiyar rawar da Matasa ke takawa wajen cigaban al'umma, don haka gwamnati  za ta tabbatar da matasa na samun horo yadda ya kamata, da bunkasa walwalar su, da samar da ayyukan yi, ga matasan Najeriya. Da yake jawabi a taron da suka gudanar, a birnin Legas, Tukura ya ce wannan matakin ya biyo bayan tuntubar, iyaye da jagororin al'umma, ya kara da cewa matasa za su marawa gwamnatin baya, tare da fatan za a yi nasara la'akari da kwazon su da biyayyar su ga shuwagabanni.

Zamu Tabbatar Da Jindadi Da Walwalar Matasa----Honarabul Kabir Tukura
Hon. Femi and Takura

Zamu Tabbatar Da Jindadi Da Walwalar Matasa----Honarabul Kabir Tukura, 

Daga Abbakar Aleeyu Anache, 

Dan Majalisar wakilan tarayyar Najeriya, mai wakiltar kananan hukumomin Zuru, Fakai, Danko Wasagu, da Sakaba, dake jihar Kebbi, kuma Shugaban Matasan 'yan majalisun Najeriya, da kwamitin Shari'a.

Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya tana sane, da irin muhimmiyar rawar da Matasa ke takawa wajen cigaban al'umma, don haka gwamnati  za ta tabbatar da matasa na samun horo yadda ya kamata, da bunkasa walwalar su, da samar da ayyukan yi, ga matasan Najeriya.

Da yake jawabi a taron da suka gudanar, a birnin Legas, Tukura ya ce wannan matakin ya biyo bayan tuntubar, iyaye da jagororin al'umma, ya kara da cewa matasa za su marawa gwamnatin baya, tare da fatan za a yi nasara la'akari da kwazon su da biyayyar su ga shuwagabanni.

Tukura ya bayyana gamsuwar sa kan tsarin tare da taya gwamnatin Najeriya murnar samun wannan matakin domin tabbatar da jindadi da walwalar matasa, 

A lokacin kaddamar da wani shiri na taimakawa matasa wanda ya gudana, a birnin Legas, Tukura, ya ce wannan tsarin zai rika taimakawa, Matasa dubu 20, da suka kammala jami'a a gurabe, daban daban, a kowacce shekara,

Wannan shirin zai taimakawa matasa samun aikin yi na hadin gwiwar gwamnatin Najeriya, 

Yayin da yake yabo Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, ya jinjinawa gwamnatin Najeriya ya kuma jaddada cewa gwamnatin Najeriya zata cigaba da daukar duk wani matakin kyautatuwa da walwalar matasa da cigaban su dama karfafa musu gwiwa a fadin Najeriya