Gwamnatin Sakkwato Ta Sanya Harajin Kan Masu Acaɓa Da Keke Napep
Gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Aminu Waziri Tambuwal ta bayyana cewa daga Litinin ta wannan Sati ya zama dole ga duk wani mai sana'ar Acaɓa da tuƙa Keke Napep da ya biya haraji a kowace rana ta Allah.
Shugaban masu tattara haraji na jiha Alhaji Aminu Dalhatu Zurmi ya bayyana cewa masu Mashin za su dinga biyan N70 a kowace rana. A yayin da su kuma masu Kekenapep zasu biya N120 a kowace rana ta Allah.
Ya ce naira 20 da aka ɗaura sama ta ƙungiyoyinsu ce domin gudanar da aikinsu.
Ya ce an yi haka domin bunkasa tattalin arzikin jiha.