Matsalar Tsaro:Kungiyoyin Matasa Masu Kishin Sakkwato Sun Yi Karatun Kur’ani
Kungiyoyin Matasa masu kishin jahar Sakkwato sun halllara a Masallacin Sarkin Musulmi Abubakar III da yammacin Lahadi bayan Sallah La’asar suka yi Karatun Alqur’an Maigirma bayan an kammala aka yi Addu’o’i na Musamman da rokon Allah domin Samun saukin wadannan fittinun da suke faruwa a Jahar na Kashe kashen Jama’a.
Ayankunan Sabon Birni, Isa, Rabah, Goronyo,Wurno da Sauran sassan kasar nan Nijeriya zubar da jini ya zama ruwan dare.
Matasan sunyi kira ga mahukunta da su yi gaugawar daukar matakin akan wannan Matsalar da ta addabi mutane ta hana kwanciyar hankali a cikin al’umma.
Daga M A FARUK SOKOTO





