An Kama Waɗanda Ake Zargi Da Kashe Kwamishina a Katsina

An Kama Waɗanda Ake Zargi Da Kashe Kwamishina a Katsina
'Yan sanda Jihar Katsina ta kama wasu da take zargi da hannu a kisan Kwamishinan Kimiya da Fasaha na Jihar Katsina Dokta Rabe Nasir da aka kashe a asubar Alhamis a rukunin gidajen Fatima Shema.
 Kwamishinan 'yan sandan Sanusi Buba ya ce, sun fara kama wasu da ake zargi da hannu akan mutuwar Kwamishinan wanda a halin yanzu gawarsa ke ma'ajiyar aje gawa dake babbar asibitin Katsina. 
Kwamishinan ya ce, jami'ansa suna ƙoƙari a binciken da suke yi na ganin an zaƙulo masu hannu kan lamarin.
 Za a yi janaza margayin a gobe Jumu'a kamar yadda addini musulunci ya tanada.