Ina Son Mijina Ya Sake Ni Don Yafi Son Kare Da ni----Matar Aure Ta Gayawa Kotu

Ina Son Mijina Ya Sake Ni Don Yafi Son Kare Da ni----Matar Aure Ta Gayawa Kotu
Wata matar aure mai neman saki, Rashidat Ogunniyi, ta shaidawa wata ƙaramar kotu  a Jihar Legas a yau Alhamis cewa mijinta ya fi son karen sa da ita.
Rashidat, 'yar shekara 40 da haihuwa, wacce ta ke neman da a kashe aurenta na tsawon shekara 12, ta shaidawa kotun cewa mijin nata, mai suna Kazeem, ya fi damuwa da walwalar karen sa da ita.
"Kazeem ba shi da kirki. Ba ya kula da ni da ɗiyana  kuma ba  ya ƙaunar mu.
"Shi kawai ya fi damuwa da lafiya da kuma walwalar karen sa. Kullum cikin yabon karen ya ke," in ji Rashidat.
Rashidat, mai sana'ar kasuwanci ta ƙara da cewa Kazeem mafaɗaci ne, "ya maida ni kamar jaka, kullum jibga ta ya ke ko yaya na ɗan ɓata masa rai.
"Akwai ma ranar da ya doke ni a gaban mutane har ya yayyaga min tufafi," in ji Rashidat.
Hakan ne ya sanya Rashidat ɗin ta roƙi kotu da ta kashe auren nata da Kazeem, in da ta ce son sa ya fita daga ran ta.
Kamfanin Daillancin Labarai na Ƙasa,  NAN ya rawaito cewa Kazeem ba ya kotun lokacin da Rashidat ke wannan ƙorafi, kuma an kai masa sammaci sau da dama amma ya ƙi zuwa.
Abin jira a gani matakin ƙarshe da kotu za ta ɗauka kan ƙorafin ganin mijin ya ƙi girmama kotu.