Kotu ta dakatar da gwamnatin Adamawa karbar fiye da Naira 500 harajin shanu

Kotu ta dakatar da gwamnatin Adamawa karbar fiye da Naira 500 harajin shanu

Wata Babban Kotun jihar Adamawa mai lamba 05 wanda ke zamanta a Yola babban birnin jihar ta dakatar da yunkurin da gwamnatin jihar ta yi na kara kudin haraji daga dari biyu zuwa dubu 3000.

Mai shari'a Justic Musa Usman ya Umarci Gwamnatin Jihar Adamawa da ta Dakatar da Karban Kudin Haraji fiye da Naira 500 

Biyo bayan shigar da kara da Kungiyar masu Dillalan dabbobi suka shigar gabatan ta na kalubalantar Gwamnatin Jihar, da hukumomin jihar, da Antoni Janar na Hukumar shigar da Kudin harajin jahar, da kuma Kwamishinan 'yan sandan jihar da baban Jami'in hukumar tsaro ta Civil Defense ta Jihar Adamawa, kamar yadda wakilin Yola24 ya ruwaito.