Yunwa a Sakkwato Gwamnati za ta fara sayar da shinkafa da rahusa
Gwamnatin jihar Sakkwato ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta ƙara azama a ƙoƙarinta na karya farashin kayayyakin abinci na yau da kullum.
Gwamnatin ta fara shirin sayo tirelolin shinkafa 300 tare da sayarwa mutanen Sakkwato a farashi mai rahusa.
Kwamishinan kananan hukumomi, Ibrahim Adare ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartaswa ta jihar ranar Laraba, 14 ga watan Agusta.
Ya ce gwamnatin Ahmed Aliyu ta damu matuƙa da halin kuncin da al'ummar jihar ke ciki ciki har da mazaunan jihar Sokoto za a sayarwa kowa ba tare da nuna bambancin jam'iya ba.
Ibrahim ya ce gwamnatin jihar ta amince da sayen tireloli 300 na shinkafa wanda za a sayarwa mazauna jihar a kan rangwame kusan kashi 45% daga farashin kasuwa.
“A ƙoƙarin sauƙaƙa wa al'umma gwamnatin jihar Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmed Aliyu, ta yanke shawarar sayo tireloli 300 na shinkafa."
"Za a tura shinkafar zuwa kowace gunduma, kamar yadda muka sani muna da gundumomi 244 a Sakkwato, kowace gunduma za a tura mata tirela daya, kuma za a sayarwa mutane a farashi mai rahusa.
"Gwamnati za ta biya tallafin kusan kashi 55 cikin ɗari. Idan farashin buhun shinkafa N86,000 ne a kasuwa, za mu samar da ita a tsakanin N40,000 zuwa N45,000.” Ibrahim Adare.
Kwamishinan ya ƙara da bayanin cewa tallafin na kowa da kowa ne, babu batun banbancin kabila ko jam'iyyar siyasa.
managarciya