A lokacin da Kasuwar Sakkwato  ta kone gaba daya a cikin wata shida na gyarata----Bafarawa

Tsohon gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi kira ga mutane su zama masu akida da daukar kaddara a rayuwa ba wai su rika yawo a tsakanin shugabanni ba, “Dana kare mulki aka koma wurin Wamakko da ya kammala wa’adinsa aka koma wurin Tambuwal mutane sun zama bas u daukar kaddara ba akida”

A lokacin da Kasuwar Sakkwato  ta kone gaba daya a cikin wata shida na gyarata----Bafarawa

Tsohon gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi kira ga mutane su zama masu akida da daukar kaddara a rayuwa ba wai su rika yawo a tsakanin shugabanni ba, “Dana kare mulki aka koma wurin Wamakko da ya kammala wa’adinsa aka koma wurin Tambuwal mutane sun zama ba su daukar kaddara ba akida”.

Tsohon gwamnan ya yi wannan bayanin ne a lokacin da shugabannin kungiyar ‘yan kasuwa suka ziyarce shi a gidansa dake birnin jiha ya ce “A lokacin da kasuwa ta kone wata shidda ko bakwai ya rage na kare gwamnati amma na yi tsaye sai da na gyara ta a kullum ina wurin, miliyan 200 na bayar kawai a share tattakar kasuwar don kasuwa ce ta ‘yan kasuwa”, a cewar Bafarawa.

Ya ce yanzu gobara ta zo a yi shawarar yanda jihar za ta ci gaba don yana bukatar yanda jiharsa za ta ci gaba dole sai da hada kai.

“Ni na gama siyasa wallahi wallahi kowane mukami ne ban son a nada ni ban son a zabe ni, a jiye hasada a bi hanyar da za a taimaki jihar nan mu hada kai mu yi kishin Sakkwato”, in ji Bafarawa.