Ana zargin Wata matashiya da yiwa kawarta yankan rago a kano

Ana zargin Wata matashiya da yiwa kawarta yankan rago a kano
Ana zargin Wata matashiya da yiwa kawarta yankan rago a kano
 

Wani kazamin lamarin ya faru a unguwar shekar maidaki dake cikin kano in da wata matashiya mai suna Aisha kabiru ake zargin  rigima ta hada su da kawarta  Bahijja Abubakar daga bisani bayan an raba su ake zargin ita Aisha taje ta dauko wata wuka ta soka Mata ita Kuma daga bisani rai yai halinsa
Bayan ta yi wannan aika-aikar  ta ranta ana kare domin a tunaninta gudun ne zai ba ta damar tsallake tuhuma da hukuncin abin da ta aikata.
Rundunar Yan Sandan kano sun Sami Nasarar cafke wadda ake zargin  harma kakakin Rundunar wato DSP Abdullahi Haruna kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

A yanzu mutane sun zuba ido domin sanin dalilin da ya sanya yarinyar daukar wannan kazamin mataki.
Managarciya tana bin lamarin don samo sahihin bayani kan abin da ya hada su wasu na fadin sarauyi ne ya shiga tsakaninsu har hakan ta faru.

Daga Aminu Abdu Baka Noma