2023: Masu ƙona mana ofishi basu isa su hana mu yin zaɓe ba -- INEC

2023: Masu ƙona mana ofishi basu isa su hana mu yin zaɓe ba -- INEC

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce hare-haren da ake kai wa ofisoshin hukumar a wasu sassan kasar nan ba zai hana ta gudanar da babban zaben 2023 ba.

Yakubu ya bayyana hakan ne a yau Talata a Abeokuta yayin wani rangadin tantance ofishin INEC da wasu ɓatagari  su ka kai hari tare da kona su, ya kuma bayyana masu kone-konen a matsayin “masu yi wa demokradiyya zaton ƙasa  da kawo koma-baya.”

A ranar 10 ga watan Nuwamba ne ‘yan bindiga suka kona ofishin hukumar da ke Iyana, a karamar hukumar Abeokuta ta Kudu, tare da lalata sama da katunan zabe na dindindin 65,000 da masu su ba su karba ba.

Shugaban INEC ya ce hukumar ba ta ji dadin ayyukan masu kone-kone ba, yana mai cewa an kai hari a wurare biyar a fadin kasar cikin watanni hudu da suka gabata.

Ya ce tuni hukumar ta fara kokarin maye gurbin kayayyakin da gobarar ta ƙone.

“Dalilin ziyarar da muka kai wannan ofishin shi ne domin mu kara tantance irin barnar da aka yi da kuma saduwa da ma’aikatanmu musamman a inda suka koma a Oke-Ilewo domin kara musu kwarin gwiwa.

“Kuma don tabbatar wa al’ummar Abeokuta ta Kudu cewa duk da wannan abin takaici, za a gudanar da zabe a kananan hukumomi a 2023.