ƘADDARA TA: Fita Ta 18
ƘADDARA TA
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 18*
*wayyo hanuna jama'a na gaji, gaskiya nayi kokari free pages dayawa haka? nayi kokari ko? to fa anan na kawo karshen free pages akwai complete kamar yadda muka saba ₦400 ne account 6037523268 Hauwa shuaibumapi keystone idan baki shirya ba dan Allah ki ragemin aiki kada kimin magana se kin shirya*
~Tana fita a guje ta shiga ɗakinsu da meenat, rufe kofan tayi ta jingina tana haƙi, tunda take bata taɓa ganin abin tsoro irin wannan mutumin ba, da kyar ta lallaɓa ta kwanta, a ranan sai bacci ɓarawo ne ya saceta.
washe gari sun idar da salla ta fito kenan zata fara aiki sabida ta riga ta saba da aikin waya taji Aneeta tana yi tace "tabbas yau zai mutu bama shi kaɗai ba duk gidannan yau zasu mutu harda ni domin yau shine karshen fansan ran yayata da suka kashe wallahi saina kashemu duka fatana ki kulamin da momy na kin san halin da take ciki idan har na mutu nima ki kulamin da ita"
dafa kirji Asmeeta tayi jin abinda ta faɗa, gani tayi ta sauka taje kitchen da kanta tayi breakfast ta jera a dinning bayan ta zuba poison ɗin da tasan babu me ci ya rayu, murmushi takeyi sannan ta share hawaye tace "ba zan zuba ido ina ganinku kuna walwala ba dole na ɗau fansan ran unty zeenat yayata wacce nafi kowa so a rayuwata"
Asmee shiru tayi tana jinta amma ta ɓuya ta yadda ba zata ganta ba, bata matsa a wajen ba har suka fara fitowa harda mai martaba ya fito domin yin breakfast, hameed yayi masifan kyau cikin manyan kaya yau sai ya fito asalin yarima hameed, yayi shirin zuwa company sabida a shirye yake yanzu ya fara kula da komai kamar yadda ya saba, a dinning suka zazzauna harda Asmeeta wacce tayi kamar itama yanzu ta fito, sultan ya gaisheta ta amsa tana mishi fara'a sannan ta gaida su ammi suka amsa, Aneeta ce ta fara zuba abincin sannan taja a gabanta kamar da gaske wai zata fara ci, da kallo asmee ta bita taga ta cika cokali bata kai baki ba tana kallon kowa daya zuba, hameed ne yasa cokali kusa da bakinshi zaici asmee ta bige, abincin ne ya zube kasa, wani kallon da yake mata yasa tace "kada kaci akwai guba a abincin"
duk suka kalleta da mamaki, Aneeta tace "guba kuma? kece kika zuba?"
murmushin gefen baki tayi sannan tace "bani bace amma inada tabbacin akwai me son ɗaukan fansa a gidannan kuma da alama kisa meshi yakeson yayi"
cikin fusata tace "me kike nufi? kina nufin nice na zuba guda a abincin?"
taɓe baki tayi tace "me yasa kika tsargu da wuri haka?"
kuka ta fashe dashi tace "wallahi ba zan jure ganin ƴar aiki baiwa tana faɗamin abinda taga dama ba"
ya kaseem yace "meeta meyasa kika faɗi haka?"
tashi tayi tace "ina zuwa ya kaseem amma kafin na dawo dan Allah kada kowa yayi kuskuren cin wannan abincin"
fita waje tayi ta ɗauko wani ƙaramin ɓera daya taƙura musu a ɗakin bayin da take kwana a baya, zuwa tayi dashi a tsorace take dashi amma saida ta shigo dashi, abincin ta ɗiba ta zuba a kasa sannan ta aje ɓeran, ci ya fara, saida ya cinye ya juya zai gudu sukaga ya kasa gudu, birgima ya fara bakinshi yana kumfa, ya kaseem yace "tabbas guba ne a abincin"
ta kalli Aneeta sannan tace "itace tasa guban ina kallonta ta zuba"
a fusace anneeta ta tashi ta shaƙe wuyanta tace "me zaisa na kashesu? me zaisa na kashesu har dani kuma zanci abincin"
kwace kanta tayi ta ciro hoton data ɓoye ta nuna mata sannan ta nunawa kowa da yake wajen tace "ga dalilin da zaisa ki kashesu harma da kanki"
hameed a firgice ya tashi yace "zeenat anneeta"
karɓan hoton yayi yana kallo yace "me haɗinki da zeenat?"
cikin bushewan zuciya tace "yayata ce"
duk wajen tsaban shocking sun kasa magana, hawaye masu zafi suka fara zuba daga idanunta tace "eh gaskiya Asmee take faɗa na zuba guba a wannan abincin kuma banyi nadama ba, kasheku nakeso nayi so nake ku mutu ku duka kuma koda nima na mutu ban damu ba"
maruka hameed ya kikkifeta dashi, yace "meyasa kika ɓoye mana? meyasa kikayi karya kikaci amana?"
kamar yadda yake maganan da zafin rai itama da zafin rai tana kallon cikin idonshi tace "kai har kanada bakin magana hameed? har kanada bakin magana kace nayi karya ko cin amana bayan kaine ka kashe yayata zeenat da hanunka"
nuna kanshi yayi da alama yaji ɗacin maganan sosai sabida fuskanshi ya nuna, yace "ni? ni na kasheta?"
tace "an gaya maka ban sani bane hameed? zeenat ta soka kamar ranta amma sabida ka tsaneta kasa wuta a ɗaki ta ƙone tana ihu tana neman taimako amma kuna ji kuna gani kuka barta har saida ta mutu a wannan ƙazamin ɗakin naka da nake danne zuciyata ina kwana a ciki tareda kai wanda banida makiyi a duniya kamar kai"
cikin ɗacin rai da hawaye tace "kasan zafin da nakeji a kowane lokaci idan na kalli wannan fuskan naka kuwa hameed? ji nake kamar nasa wuƙa na rinƙa caccakan zuciyarka har sai naga ka daina nunfashi, hameed na tsaneka kuma wallahi ban karaya ba saina kasheku gaba ɗaya kamar yadda na kashe Amrah na kashe fauza wanda suke niyan tonamin asiri"
kaseem yace "me suka miki da zaki kashesu? kece kika kashe Amrah?"
tana kallonshi ido cikin ido tace "eh nice, nice na kasheta"
maruka masu zafi yayi mata sannan yace "me suka miki?"
tana dafe da kunci har hulan kanta ya faɗi tace "sabida suna son mutanen gidannan kuma duk wanda yaso koda ɗaya daga cikin mutanen gidannan ne har abada ya zama abokin gaban ANEETA LAWAN LAMBA"
hameed rike kanshi yayi jin asalin sunanta, ta juya baya tace "wannan masarautan me ɗauke da hakkin mutane ba zaku taɓa jin daɗin zama a cikinta ba, domin daga wannan masifan ya mutu sai wani masifan ya kara zuwa muku no peace for a wicked"
share hawaye tayi tace "ni ƴar sarki ce na taso a gidan sarauta amma na koma ƙasar waje da zama sabida business ɗina amma sabida ku na zubar da komai na dawo, kukasa na kashe mata da miji da ɗansu a matsayin iyayena da nayi accident dasu"
hameed yace "meyasa ban taɓa saninki ba duk da ke kanwar zeenat ce?"
tace "kamar yadda baka taɓa son zeenat ba hakan shiyasa ba zaka taɓa sanina ba, ya nace mata karta kuskura ta nuna maka ni kanwarta ce idan ba haka ba zan iya daina magana da ita kuma tasan zan iya, amma daga karshe shine kuka kashemin ita harma da jaririyarta"
cikin zafin rai yace "yau zaki bar gidannan Aneeta yau zaki bar gidannan ko kwana ɗaya ba zaki kara ba"
tace "sai me? kana ganin koda nayi nesa daku zan kyaleku ne? wallahi saina kasheka kamar yadda ka kashe zeenat"
yace "bani na kasheta ba kuma ki fita ki bar gidannan"
a zafafe ya riketa yana janta, tirjewa take tana cewa "koda na fita ba zan barku ba"
buɗe kofan yayi yace "na sakeki saki ɗaya, na sakeki saki biyu, na sakeki saki uku"
wurgi yayi da ita cak ta faɗa akan hanun wanda ya shigo yanzu sanye da bargon kanshi har yanzu a rufe, wari ne ya ziyarcesu jin warin duk suka kalleshi, cikin muryanshi me tsoratarwa yace "ni na aureki, oh sorry ni zan aureki tunda ya sakeki"
riketa yayi ya ɗaga bargon ya buɗe fuskanshi, a razane Asmee take kallonshi ganin tsananin kama da yake da hameed duk da tarin sajen da yake dashi wanda yake da datti hakan bai hana kama sosai da sukayi ba, murmushi yayi mata baƙaƙen hakoranshi suka bayyana, Aneeta murmushi tayi, hameed ya koma bayan Abi ya ɓuya, harda Abi jikinshi rawa yake yi, hanunta ya rike ya karaso da ita ciki, yace "wannan itace matar da zan aura sunanta Aneeta lawan lamba"
ammi a tsorace tace "ABDULHAKEEM"
dariya yayi sosai har saida suka koma baya sannan ya ɓata rai yace "na'am Ammi"
sultan ɓuya yayi a bayan ammi kamar yadda meenat ma ta ɓuya, ya kalli hameed dake bayan Abi yace "my twin bro ba zakamin welcome bane?"
jikin hameed ya fara rawa, girgiza kanshi yayi ya maida tulin gashin kanshi me uban dattin baya sannan yaja wandon da yake faɗuwa a jikinshi yace "ya kamar babu wanda yayi murnan dawowa na ne?"
ganin basu amsa ba ya kara kwashewa da wani dariyan, Asmeeta baya tayi cikin tsoron da bata taɓa ji ba a rayuwarta, ya kalli ɗakin sosai sannan yace "komai ya canja amma duk baku canja ba"
Abi sai yanzu ya iya buɗe baki yace "waya buɗeshi?"
shiru sukayi harda Asmee wacce ta gama firgita, ya daka tsawan da yasa ɗakin girgiza yace "waya buɗe hakeem nace?"
kallon Asmee hakeem yayi a tsorace ta sunkuyar da kanta jikinta kamar mazari, hakeem ya kaikaya bayanshi dake kaikayi sannan yace "wanka nakeso nayi sannan naci abinci na samu na hau gado na huta, bayan na taso sai a bani sandan sarautata wato a matsayina na YARIMA HAKEEM ɗan sarki Abdallah me jiran gado, idan an bani sandata zan shirya na tafi babban company ɗinmu na diamond wato ABDOOL DIAMOND COMPANY nawa ni Abdulhakeem da twin bro ɗina Abdulhameed"
kallon Aneeta yayi ya mika mata hanu yace "baby let's go"
hanunta ta ɗaura a nashi ya rike yana kallon Asmeeta data kasa maida idanunta daidai, yana hura whistle ya fara taka stair cikin isa da gadara da izza, bargo me dattin yana binshi a baya domin bai rufu dashi me kyau ba.
Abi yace "hakeem dakata"
tsayawa yayi ya ɗagawa abi gira yace "yes"
hawa stair Abi yayi ya fara jan hanunshi ya sauka dashi yace "fita ka bar gidannan"
yace "dad nan ba gidan ubana bane? ba nine yariman wannan garin ba? meyasa kake korata haka kamar kare?"
Abi cikin zafin rai yace "ka fita ka bar gidannan nace"
Ammi ce tazo ta tsaya a tsakaninsu tace "babu inda zaije shima ɗane kamar kowa a wannan gidan yadda hameed yake shima haka yake, ko ka manta tare aka haufesu a rana ɗaya a lokaci ɗaya?"
Abi yace "ki...."
hanu ta ɗaga mishi tace "wannan karon ba zan sake bari ayi kuskure ba, ina tare da hakeem koda kasheshi za'ayi saide a kashemu tare, sannan kamar yadda ya faɗa za'a bashi yarima sabida dama nashi ne, sannan zai fara zuwa company ɗinsu na harkan diamond sabida sunansu ne a kai ko manta ranan daka buɗe musu kasa Abdool sabida shine farin sunansu su duka biyu meyasa yanzu kuma zai fasa zuwa? wannan karon ba zan bari a cutar dashi ba, duk abinda yake so nima inaso"
hanun Aneeta taje ta rike tazo ta haɗa dana hakeem ɗin tace "koda ko abin zai zama ajalina ne"
rike da hanun hakeem dana Aneeta take tafiya har ta haura zata shiga ɗaki tare dasu Abi be rufe baki ba yana kallonsu.
kaseem ne ya dakatar dasu ta hanyan cewa "to ai ba hameed bane ya kashe zeenat nine na kasheta"
tsayawa sukayi su duka, Abi ya kalleshi sannan yace "me yasa zaka ɗaurawa kanka abinda bakayi ba? ni nan nine na kashe zeenat na hanuna"
meenat tace "Abi nasan kana faɗan haka ne domin ka ciremu daga matsala amma kowa yasan nafi kusanci da unty zeenat nice na kasheta da waɗannan hannayen nawa"
sultan ya ɗauke meenat dake gefenshi da mari yace "yaushe kika kasheta? ai kowa ya ganni lokacin dana kasheta kowa shaida ne"
hameed yace "ku daina wannan karyan ni hameed nine na kashe matata zeenat da kaina"
dariya hakeem yayi kamar zai fasa gidan da dariya sannan ya shige ɗaki.
hameed kuka ya zauna ya fara yi, a hankali Asmeeta taje tana cewa "kayi hakuri ka daina kuka"
ji tayi ya rungumeta kam kam kamar wani zai kwace mishi ita, ya cusa face nashi a kirjinta, yatsunta masu taushi ta cusa a gashinshi me laushi ta fara shafawa, gani tayi ya kaseem ya zauna yana furta Innalillahi, meenat zama tayi itama domin tsayuwa ba zaiyi ba, ga cikinta daya fara nuna kanshi yunwa takeji amma ta kasa yin komai, sultan kuka yake yi shima me cin rai.
hakeem suna shiga ya saki hanun aneeta mannata yayi da jikin bangon ya shaƙe wuyanta, kakarin mutuwa ta fara tana kwace kanta, cikin wani irin murya yace "meyasa kike hararanta? meyasa kike hararan wannan kyakkyawar yarinyar da ko kuɗa banaso ya kalleta bale mutum ɗan adam ya harareta"
idanunta sun firfito waje tsaban karfin hakeem ta kasa koda cire yatsanshi ɗaya ne bale hanunshi duka, ammi wacce ta shiga ciki domin haɗa mishi ruwan wanka batasan me yake faruwa ba, cikin azaba ta samu tace "dan girman Allah hakeem ka sakeni ba zan kara ko kallonta ba"
sakinta yayi ya wurgar da ita, rike wuyanta da takeji kamar yana jini tayi, ta kalleshi ya fara ɓalle belt ɗin wandon jikinshi, kasa yayi da wandon da sauri ta rufe ido ta juya baya, bargon yayi wurgi dashi sannan ya cire rigan, saida ya cire riga farin fatarshi ya bayyana, ɗaura towel yayi a waist, faffaɗan kirjinshi ya bayyana, kiran jikinshi irin na hameed ne kamar masu gym, faɗawa yayi kan gadon wanda nashi ne asali da hameed lumshe ido yayi sannan ya buɗe a hankali jin ammi tace "ka shiga kayi wanka"
bai tashi ba kuma be amsa mata ba, kallon Aneeta da take shan ruwa tayi kamar zata haɗa da goran ruwan ta cinye tsaban ishi tayi.
shi kuma saida yaga dama kafin ta tashi ya shiga bathroom ɗin domin yin wanka, lumshe ido yayi, a duk lokacin daya lumshe ido ita yake gani lokacin da take bashi abinci da kuma lokacin da take kunceshi, wani irin smiling yayi wanda ya kara nuna asalin kamanshi da hameed kamar an tsaga kara.
cikin arrogant voice nashi yace "fine girl"
Kaseem cikin tausayi ya rungume kan hameed yana ji yana sauke ajiyan zuciya a jikinshi, Asmeeta rufe ido tayi wallahi da tasan haka da bata buɗe ba, da tasan shi ɗin bala'i ne a rayuwarsu da babu abinda zaisa ta taimakeshi harma ta buɗeshi, tayi zaton Aneeta ce ta kulleshi kuma babu wanda ya sani, a niyanta taimako ne sai gashi ya dawo tashin hankali, cikin sanyin murya yace "ya kaseem"
yace "na'am"
yana cigaba da shafa kanshi, yace "zaka kasance dani? ba zaka bari hakeem ya rinƙa tsoratar dani ba? ba zaka bari yazo wajena ba?"
cikin tausayinshi yace "eh ba zan bari ba karka damu ina tare da kai"
yace "to na gode"
Asmeeta cikin sanyin jiki ta shafa kan sultan tace "sultan ka daina kuka babu abinda zai faru"
yace "to"
share hawayen yayi, meenat kuma a wajen ta kwanta domin cikin yana yawan sata bacci amma baccin ma yaki zuwa, Asmee tace "to a cikinsu waye ya kashe zeenat? meyasa ya kasheta? me tayi? meyasa suka rufe hakeem? kuma da alama yanada kusanci da zeenat sosai to meyasa suka kasheta?"
Jiddah Ce....
managarciya