Babban Buri:Fita Ta Sha Shida

Da gudu ta nufi ɗaki ta zaro mayafi ta fito suka rankaya a guje sai cikin mota. Gudu yake yi ba sararawa ikon Allah ne kawai ya kaisa gurin lafiya. Ganin motar asibiti data ƴansada a gurin ya sanya sa saurin yin parking ya isa gurin sai dai yana kaiwa ana kulle murfin motar da aka sanya ta.

Babban Buri:Fita Ta Sha Shida

BABBAN BURI

MALLAKAR DOCTOR MARYAMAH IBRAHEEM.

SADAUKARWA GA AISHA IDREES ABDULLAHI {SHATU}.

FITOWA TA SHA SHIDA


~~~Amsa masa a kayi da "kana magana da Ayuba matar ka ta samu haɗari ne yanzu haka gamu anan.... ya gaya masa sunan gurin da suke , amman munsamu kiran jami'an tsaro suna kan hanya, idan son samu ne kamin su samu isowa ka iso....".

Bema jira ƙarshen maganar ba ya yi jifa da wayar yana mai ɗaura hannu a saman kai hankalinsa a matuƙar tashe, da gudu ya fice daga Parlourn ya hau kwaɗawa Safara'u kira dake ɗaki kamar waƴanda ke zaman makoki.

Da sauri ta fito daga ɗakin tana faɗan "daddy an gant....?"tunkan ta iyar da faɗin abinda ta yi niyar faɗa ta ganshi tsaye dukkanin hannayensa a saman kansa cike da tashin hankali ta nufi gunsa.
"Daddy lafiya?".
Cikin tashin hankali ya ce "Ina fa lafiya Safara'u? maza kuzo muje muga a wanne hali Umma take".

Da gudu ta nufi ɗaki ta zaro mayafi ta fito suka rankaya a guje sai cikin mota.

Gudu yake yi ba sararawa ikon Allah ne kawai ya kaisa gurin lafiya.

Ganin motar asibiti data ƴansada a gurin ya sanya sa saurin yin parking ya isa gurin sai dai yana kaiwa ana kulle murfin motar da aka sanya ta.

Kai tsaye mota ya koma yabi bayan motocin da suka rankaya zuwa asibiti.
A gaugau ce aka karɓeta ganin tana bukatar taimakon gaggawa, kai tsaye emergency room suka nufa da ita.

Nan suka tsaya suna jajanta abin cike da adduoi a bakinsu. 

Kusan 3hour saiga DOCTOR ya fito nurse nurse suna take masa baya.

Office ɗinsa ya nufa kana yasa aka kira masa ƴan uwanta.
Da hanzari suka nufi office ɗin , zama sukayi a saman kujerun da aka tanada domin hakan.

Gaisawa su kayi da DOCTOR sannan ya fara yi masu baya ni "a gaskiya anyi babban arziƙi , domin kuwa Allah yasa abin yazo da sauƙi, yanzu haka dai munyi mata abinda ya kamata harta samu bacci so that zata ɗauki tsawon lokaci kamin ta farfaɗo, kuma tana buƙatar kulawa sosai domin ciwon dake jikinta, gaskiya ta samu raunuka sosai sai dai muyi fatan Allah ya bata lafiya".

Da "Amin" Alh Bello ya amsa yana mai mikawa DOCTOR hannu suka yi musabaha sannan suka fito domin zuwa duba jikinta a ɗakin da aka canja mata.


A can gida kuwa hankullan mutan gidan a tashe yake najin labarin da Ƴar beauty ke bayarwa tun safe Hajiya Umma ta fita ba ganta ba, sai gashi kuma annemi Alh Bello anrasa dashi da Safara'u a cikin gidan.

Hankullan al'umma sun tashi sosai, gaba ɗayansu a filin tsakar gidan suka fiffito masu kuka na yi masu jajantawa na yi.

Ƙarfe 5pm nikam na yi masu sallama na yi gida cike da jimamin abinda ya faru.

6pm ya shiga gidan ganin ayarin ƴan gidan a waje be damesa ta gefensu ya ratsa ya wuce.

Yana batun sanya ƙafarsa cikin part ɗin Hajiya Inna ya jiyo muryar Alh Sunusi na faɗan "yanzu Haidar har ka yi girman da zaka ganmu muda iyalanmu amman ka kasa gaidamu balle ka samu zarafin tambayarmu lafiya muke tsaye anan?".

Jin abinda yake faɗa be sanya sa juyowa ba ya yi shigewarsa sashen yana me jan tsaki.

Taradda Hajiya Inna ya yi zaune a Parlour kamar kullum ya ce "meya ke faruwa ne a gidan Hajjaju?".

"Hajiya Umma ce ba'a gani ba tun safe sai kuma shi mijin nata da ƴar Safara'u da ba'a gani ba daga baya, kuma anyi kiran wayar su a kashe."

"Okey" kaɗai ya ce kana ya nufi ɗakinsa domin ya watsa ruwa.

Harya shiga ya fito da sauri ya ce "Hajiya Inna yau deejah ta shigo kuwa?", Ƙyalesa ta yi ko kallon gurinda yake bata yi ba.

Gajiya ya yi da tsayuwa ya koma cikin ɗakin jiki a sanyaye.

Bakin gado ya zauna sannan ya janyo wayarsa ya kara a kunne , cikin sa'a kuwa wayar ta ɗauki ringing.
Cike da farin ciki yake sauraren ta gunda za'a daga sai dai harta yanke ba'a ɗaga ba.

Ƙara danna wani kiran ya yi, ni kuwa lokacin ina riƙe da wayar kawai nauyi ne ya hanani ɗagawa "to nace masa me?, kishi ne ya hanani kulasa kwana biyu?", "Ina bazan ɗaga ba", na faɗa ina girgiza kai.

Wani kiran ne ya sake shigowa wayar, tana gaf da yankewa na ɗaga iname cewa "Assalamu Alaikum".

Nauyayyiyar ajiyar zuciya ya saki a bayyane wacce ni kaina sai dana ji ta.

"Kin kyauta", ya faɗa.Cikin shagwaɓar da bansan lokacin dana iyata ba na ce "dana yi me? iname ɗan turo baki gaba.

"Kinfi kowa sani ai", ya faɗa daga can. "Da yake nice sarkin lefi ko?, na faɗa iname ɗan hararar wayar.

"Bance ba kar a koma fushi dani", "yanzu me kikeyi?".

Mamaki tambayar ta bani sai kuma na basar na ce "ba abinda na keyi wani abun ne?".

"Bakomai tambaya ce nakeyi ko ban isa abani amsa ba?", "ta nawa kuma?, bancin na riga na baka amsar".

"Okey zan shiga wanka yanzunnan na dawo daga aiki, idan na fito bayan magrib ko isha'i zan kira, karfa ki kashe wayar ko na kira a ƙi ɗaga wa".

"Ɗan murmusawa na yi sannan na ce "insha Allahu ba za'ayi ko ɗaya ba , anan muka yi sallama kowa ya ajiye wayarsa.

A haka wannan daren muka kashesa da love kowa na ƙoƙari ganin ya faranta ran ɗan uwa.
Duk da be bayyana min yana sona ba amman tabbas inada yaƙinin yana sona, nima kuwa haka sai dai wani lokacin sai naga kamar na ɗauko ruwa dafa kaina ne na son wanda ya fini a komai, to a haka dai nake da *BURIN* ya zamo mallakina ni kaɗai.


★★★★★★

Sai guraren 10pm sannan Hajiya Umma ta buɗe idanuwanta ta sauke su a jikin bangon ɗakin runtse idanuwanta ta yi tana mai tunanin abinda ya faru da'ita.

Ganin ta buɗe idanuwa ne ya sanya su saurin miƙewa suka nufeta, ɗan murmushin ƙarfin hali ta yi masu wanda hakan yi ƙara ƙarfafa masu gwiwa.

Saurin fita daga ɗakin ya yi yake domin ya kira DOCTOR domin ya ce "idan ta samu farfaɗo wa a kirasa da wuri".

A tare suka shigo da DOCTOR MARYAMAH wacce itace ke dutyn dare a lokacin, wuri suka basu bayan ta gama duba ta ta fice tana meyi mata fatan samun sauƙi a gurin Allah.

Sai lokacin suka tuna da sun baro mutan gidan a cikin halin rashin inda suke.

Aron wayar ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen Safara'u ta yi ta loda number Ƴar beauty a wayar ta kara a kunnenta.

Bugu ɗaya kuwa ta ɗaga cikin dasashishiyar murya ta ce "hello" , ƙwalla ce ta zubowa Safara'u domin kuwa ko ba'a faɗa ba tasan ƙanwar tata tana cikin wani hali.

Gaya mata asibitin da suke ta yi ai kuwa a cikin daren dukkanin ƴan gidan suka rankayo domin duba lafiyar jikin Hajiya Umma.

Sosai kowa ke jajanta abin ganin yadda lokaci ɗaya halittar jikinta ta sauya .

Sai guraren 12:30am sannan suka koma gida, anaci gaba da jajanta lamarin.

Yadda suka ga rana haka suka ga dare a zaune kowa da abinda yake faɗa.

Ƙarfe 6am ya gama shirin fita aiki domin yana son ya biya asibiti dubo jikin Hajiya Umma.

Shi da kansa ya jaa mota kasancewar ta tambayi Baban Gida direba asibitin da suke.

Koda ya shiga bakowa a cikin ɗakin ita kaɗai ce kwance duk sun fita zuwa buƙato cinsu.

Bakin gadon ya nufa ganin idanuwanta biyu, gaidata ya yi sannan ya tambayi jikin nata, cikin sanyin murya take amsa masa.

Sannan ta janyo hannunsa ta riƙe a cikin nata tana kallonsa , ƙwalla ce ta silalo mata a saman kuncenta , hannu tasa ta sharce ta sannan ta yi masa nuni da ƙofa, gane nufinta ne ya sanya yaje ya kulle ƙofar daga can ya zago wayarsa a cikin aljihu ya shiga recording ya mayar da'ita aljihun wondan sa sannan ya juya ya koma gunta.

"Kallonsa ta sake yi sannan ta ce "Haidar ka yafemin , alhakin kane ke bi biyata , dani har su Alh munyi ma laifi babba, yau zan gaya maka abinda nake ganin kamar ka manta dashi".....

ƳAR MUTAN BUBARE CE