Ɗalibbai 5 daga cikin sama da 70 da aka sace a Zamfara sun samu 'yanci
Ɗalibbai 5 daga cikin sama da 70 da aka sace a Zamfara sun samu 'yanci
Aƙalla ɗalibai biyar ne ƴan makarantar jeka-ka-dawo ta gwamnati dake Ƙaya ta ƙaramar hukumar Maradun a Jihar Zamfara ƴan ta'adda suka sako.
Wani tsohon kansilan yankin Ƙaya Yahaya Ƙaya ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
A cewarshi ƴar sa mai suna Amina na ɗaya daga cikin ɗalibban da aka saki.
Ya ce ɗalibban biyar an kai su gidajensu a ƙaya da misalin ƙarfe ɗaya na tsakiyar daren alhamis.
Idan dai za a iya tunawa kwanan nan ne rundunar ƴan sandan jihar ta sanar da cewa an yi garkuwa da ɗalibban makarantar sakandiren su sama da 70.
Sai gashi labari ya zo na sakin 'yan kaɗan daga cikin yaran ba tare da jin labarin sauran yaran ba.
managarciya