2023:Yana da kyau a baiwa Malamai dama su tsalkake jihar Sakkwato

2023:Yana da kyau a baiwa Malamai dama su tsalkake jihar Sakkwato

Yau shekarana huɗu da sanin Malam Muhammad Lawal Maidoki Kuma tun sadda nasan shi har yanzu ban ji ba Kuma banga wani aibi a gefensa ba.

Shakka Babu shekarun da ya share yana jagorantar Hukumar Zakkah da Wakafi ya haifar da cigaba ga jahar Sakkwato  domin zan iya cewa hukumar wata gwamnati ce Mai zaman kanta, saboda tasirin ayyukan hukumar ga talakka.

Yau a bayar da abu domin talakkawan jahar Sokoto, su kansu za su so ace abun an kai shi hukumar Zakkah domin a raba musu, a tunaninsu sai yafi isa garesu.

Babban misali shi ne, tallafi na Dangote da BUA Wanda sanadiyar Hukumar Zakkah ya isa ga tallakawan jahar  wadanda Allah ya nufa su amfana.

Wannan nasarar duk saboda kwatanta gaskiya da amana irin na Sadaukin Sokoto, no wonder Sarkin Musulmi ya ba shi wannan sarautar saboda irin sadaukantakarsa.

Mu dawo gefen shugabanci, tun bayan rasuwar Annabi Muhammad SAW sahabbai masu illimi suka yi Halifanci, a nan Kuma daular Usmaniyya bayan wafatin Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodio masu illimi ne suke shugabanci kafin al'amura su birkice.

Dalilin wannan matashiya shine, Babu tantama Jahar Sokoto jaha ce ta addini, jaha ce da yakamata su fara tunani gwada ba Malammai jagoranci domin sauran jahohin Arewa su yi koyi.

A lokacin da jam'iyun siyasa ke lalaben ɗan takarar da zai taimakawa jahar nan da kuma ɗaukaka martabarta, ni kuma na hango wani mutum da karɓuwarsa ga talakkawa, da kuma ayyukan alkhairi da yayi haɗi da addininsa ba Gwamna ba har shugaban ƙasa ya cancanta da riƙewa.

Wannan Bawan Allah shi ne Malam Muhammad Lawal Maidoki, ko kunsan cikin fikira da baiwa da Allah ya yi masa yayi Sanadiyar Kawo abubuwan alkhairi a jahar Sokoto Kamar haka.

1. Ya sa Gidauniyar Qatar Charity ta tallafawa mata dubbai da awaki kyauta domin kiwo.

2. Ya sa Gidauniyar Qatar Charity ta gina masallatai Wanda basuda adadi a gundumomi 87 dake jahar nan.

3. Ya sa Gidauniyar Qatar Charity tana gina wata katafaren makaranta kusada RTV domin ɗiyan marasa ƙarfi da marayu a jahar nan.

4. Ya sa gidauniyar Qatar Charity ta gina ɗaruruwan gidajen a Gandi domin Samar da muhali ga 'yan gudun hijiran dake zaune a sansaninsu a garin Gandi, tare da gina masallaci, makaranta, asibiti da kasuwa a rukunin gidajen.

5. Ya sa Gwamnatin Indonishiya za ta tallafawa gwamnati Jahar Sokoto domin inganta illimin almajirrai.

6. Ya samoma Yara guraben karatu a Malaysia Kuma dukansu 'ya'yan talakkawa ne.

7. Da dai sauransu......

A jahar Sokoto ku gwadamin ɗan siyasar da ya taɓa haka.

Shifa Malam Muhammad Lawal Maidoki ya yi hakan ne saboda Allah badon yanada aniyar siyasa ba, sai ga shi hukumar da yake jagoranta ta yi tasiri ga 'ya'yan talakkawa.

Tau inama ace shi ne Gwamnan Sokoto me kuke tunani.

Shakka babu da ace Jigogin siyasan Sokoto za su yi koyi da hanyar da tsohon Gwamnan Borno Kashim Shettima ya bi domin ɗora Gwamna Babagana Zulum su ba Malam Lawal Maidoki dama, da jahar Sokoto Insha'Allahu sai tafi kowace jaha cigaba da kuma kwantata gaskiya da amana a Nijeriya.

Wannan Raayin

Isuhu Dan Mamman ne.
yousoufladan@gmail.com
isuhuladan@gmail.com