‘Yan Bindiga Sun Nemi A Ba Su Miliyan 50 Kafin Su Saki Mutum 6 Da Suka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

‘Yan Bindiga Sun Nemi A Ba Su Miliyan 50 Kafin Su Saki Mutum 6 Da Suka Yi Garkuwa Da Su A Katsina

 ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane shida a Tashan Buja dake karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Maharan sun kai farmaki kauyen ne da misalin karfe 12:30 na  daren Juma’a ba tare da harbi ba, suka dauke wata matar aure, danta da wasu mutane shida, kamar  yadda jaridar Leadership ta kalato.

Katsina Post  ta nakalto wata majiya mai tushe, wanda mazaunin garin ne, yana cewa:  “Yanzu haka daga gidan mutumin da ‘yan bindiga suka sace matarsa da dansa a daren jiya nake.

“Mutane sun ga maharan sun doshi jeji tare da wasu mutane hudu, inda ya zama shida suka yi garkuwa da su.

“Sun shigo garin da misalin karfe 12:30 na  dare, sun aiwatar da ta’asarsu shiru ba tare da harbi da zai nuna kasancewarsu a wajen.

“Yan bindigar sun zanta da Mista Musa Shaun, mijin matar da aka sace, inda suka bukaci a biya naira miliyan 50 a matsayin kudin fansarsu.”