ANA BARIN HALAL...:Fita Ta 20
ANA BARIN HALAL...
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*PAGE* 20
*MUKHTAR GARBA (M.G)*
Shine cikakken suna na, gidan mahaifina yana unguwar kobi da ke cikin garin bauchi, mahaifiyata Fatima wacce muke ƙiranta da suna Goggo mu bakwai ta haife mu, yaranta guda shida manyan uwa ɗaya uba ɗaya suke,nine autan su wanda kuma mahaifina daban da su, gaba ɗaya yaranta maza ne, bata taɓa haifan ƴa mace ba, Malam Garba shine sunan mahaifin yayuna wanda nima da sunan nake amfani da shi, malam Garba malamin makaranta ne a *KOBI PRIMARY SCHOOL* unguwa ɗaya suke da mahaifiyata, auren soyayyah sukayi da Goggo, Goggo nah faran macece bafulatana ƴar *KAFIN MADAKI* amma girman garin bauchi, sunyi zaman lpy da mijinta malam Garba da ƴan uwan mijinta sosai, kuma babu laifi suna rayuwar su cike da rufin asiri, Babban wanmu sunan shi
Auwal, sai Sani, Salisu, Rabi'u, sai twins da tayi na ƙarshe wato Hassan da Hussain, gaba ɗaya tsakanin su shekara bibbiyu ne, ƴan biyun suna da shekara biyu mahaifinsu Allah ya mishi rasuwa, lokacin yayah auwalu yana da shekara goma, yayah sani takwas, salisu shida, yayah rabi'u huɗu, yayah hassan da hussain kuma suna shekara biyu, domin an yaye su suna tafiya ko ina da ƙafan su, dukkan su kuma farare ne sol kaman mahaifiyar mu, gashi kowa a cikin su yana hanci tamkar na goggo, sai dai kamanin su ɗaya da mahaifin su, Yayah Hassan da hussain ne kawai suka ɗauko fuskan Goggo sak, mijin goggo ya rasu ne sakama kon ciwon wuni ɗaya tak, a yanda ake bani labarin mutuwan ya bugi jama'an da suke cikin gidan, domin gidane mai girman gaske a kobi, shashi- shashi ne a gidan, gidane daya ƙunshi family dayawa, gashi malam Garba mutum ne na kowa, gashi baida tashin hankali yana zaune lafiya da kowa, bayan rasuwan shi da kwana goma mahajjata suka dawo lafiya cikin ƙasashen su, wanda yayi daidai da dawowan ɗan'uwan shi da suke ƴaƴan bappanu, kuma sun tashi sa'o'i juna, akwai shaƙuwa mai yawan gaske a tsakanin su, wato *ALHAJI ALKALI ABDULLAHI* haka ya samu jagorancin ƴan'uwa da abokan zumunci har zuwa sa shin mahaifiyar malam Garba, hannun shi riƙe da na yayah salisu da yayah rabi'u, bayan shi kuma su yaya auwal da yayah sani ne ke biye da shi da sauran ƴan rakiya, kuka sosai yayi a ɗakin Inna, domin itama ganin shi sai duk hankalin ta ya tashi tayi ta kuka ana bata haƙuri, alkhairi sosai ya ajiye mata ya koma jaddada mata insha Allahu babu komai zai kula da su, daga nan ya taho ɗakin goggon mu, nan ma ansha kuka ba kaɗan ba, domin tsakanin Alkali Abdullahi da Malam Garba akwai shaƙuwa sosai, duk da yayi kuɗi baida makusanci irin malam Abdullahi, duk da matan shi basu so, domin gani suke ajin mijin su ya wuce na tarayyah da malam Garba, amma furr ya nuna musu basu isa ba, sudai suna zumumcin su, amma matayen su basa zumumci, gara ma uwargidan wani lokaci ta kan leƙo goggo, irin ko anyi rasuwa ko ta haihu ta shigo tayi barka, itama ko suna bata shigowa, amma takan dai ɗan leƙo, ita ƴa ɗaya ta haifah wanda a lokacin ta kai shekara shabiyar, domin Alƙali ya riga malam garba aure, kuma tun da ta haifi ƴarta mai suna safiya ta samu matsala a mahaifanta bata sake haihuwa ba, safiya na da shekara uku Alƙali ya ƙara aure na biyu, ita amaryar tana isa da izzah domin ita ƴar cikin fada ce, tana ji da sarauta ita ko ɗaga kai ta kalli mutane da mutunci batayi,
Tana da shekara ɗaya ta haihu ɗa namiji, bayan shekara ta ƙara ɗa namiji, wanda tare aka haife su da yayah auwal, na uku sa'an yayah sani ne shima namiji, lokacin alƙali ya ƙaro wata ƴar wani Ambasoda tana karatu a Bacas, itama tunda tazo ta haifi nata yara mata guda biyu alokacin, a wannan lokacin ne malam garba Allah yayi mishi rasuwa.
Alƙali yayi kuka sosai ana bashi haƙuri, daga nan ya tafi, bayan tafiyan shi aka shigo da kayan abinci sosai gidan, inna tazo har gefen Goggo ta raba abincin biyu ta ɗauki ɗaya ta barwa goggo ɗaya, daga wannan lokacin Alƙali ya an bawa yaya auwal kuɗi idan an kwana biyu a shigowa goggo da shi, tana arba'in ma ya sake haɗo kayan abinci aka kawo,.
Haka dai rayuwa tayi ta ja har goggo ta ƙarashe takaba, Alƙali bai gajji da hidima da su ba, makarantan da Malam Garba wanda ake ƙiran shi da Baba suka cigaba da ɗaukan ɗawainiyar karatun su yayah na, bayan shekara aka saka su yayah hussain a makaranta, sannan a wannan lokacin Alƙali ya bijiro da maganan auren Goggo, innah kuwa tayi ruwa tayi tsaki ta dage akan sai anyi, domin maganan gaskiya ta hanga ta hango babu wani tsayayye da zai iya cigaba da kula da su irin shi, kuma idan goggo tayi aure duk watsar mata da yara zatayi, don babu mai iya riƙeta da yaran nan, matan Alƙali kaman zasuyi ƙaramin hauka da sukaji maganan auren nan, domin maganan gaskiya Goggo irin kyawawan matan nan ne, wanda kyaun su yake firgita mutum, amma babu yadda suka iya Allah ya nufa akwai rabon haihuwata a gidan dole sai Goggo taje, ya ɗago kai ya kalle ni bayan ya faɗi hakan, nima ɗagowa nayi na kalle shi, amma lokaci ɗaya sai naji jikina yayi sanyi saboda ban taɓa ganin rashin murmushi a fuskar shi ba sai yau, fuskan shi na kallah sai naga kaman shi da A.G yau, kamane bawai kaman hanci ko ido ko wani abu ba, kama ne dai kaman na yanayi, juyar ds kai na nayi na kalli gefen da su yayah suke zaune, abun mamaki karaf idon mu ya haɗe da na A.G, ya ɗan kwantar da kanshi saman kujeran da yake yana kallon mu, yayah Ahmad kuwa suna ta hira da Aunty J, kawar da kaina nayi da ɗan sauri ganin ƙura min ido da yayi, kallon na yar kan M.G, ajiyan zuciya ya sauƙe bayan ya ajiye ruwan da ya ɗauka ya sha.
Ranan jumma'a aka ɗaura auren su a babban masallacin jumma'a da yake ƙofar fadan bauchi, kuma a ranan Goggo ta tare gidan ta, Baba nah yaso goggo ta tare da dukkan yaran nata, amma inna ta hana kan, cewa tayi daga baya za'a kawo ƴan biyu da Rabi'u, sauran kuma zasu zauna anan, tunda gida biyu ne tsakanin gidan Baba na da gidan mu.
Tunda ga ranan da Goggo ta shiga gidan auren ta bata samu nutsuwa da kwanciyar hankali ba, dukkansu matan gidan da yaran gida haɗe mata kai sukayi suka hanata sakat a cikin gidan, hattah da masu aikin gidan basu ganinta da mutumci ko girma, don ko aikin gidan Uwargida (hajiya hauwa) bata amince a ringa yi mata ba, sannan yaranta rabiu da ƴan biyu sun sha wahala da dukan gaske a hannun ƴan gidan, har ta kai zaman su yafi ƙarfi a chan wurin Inna, yawanci sai kwanciya ke dawo da su gidan, ranan girkin Goggo kam ma achan gidan mu suke kwana a ɗakin Inna cikin kulawan Yayah Auwalu, Baba na duk yadda yaso ya bada kulawa wa goggo na da ƴan'uwa na abu ya gagara, Goggo tasha wahala a hannun kishiyoyinta har tsawon shekara uku Allah ya nufa ta samu cikina, laulayin da Goggo tayi ya wuce tunanin mai tunani, don ko ruwa bata isa tasha ba sai ta dawo da shi, abun da yake iya zama a cikinta shine ruwan sirki wanda Inna ke aiko yaya Auwalu ya kawo, domin shi kaɗai ne yake shigowa gidan basu hantare shi ba, don shi babu fuskan rainia tare da shi, cikina yana wata uku bai cika huɗu ba Baba na ya saki Goggo, babu wanda ya isa yace ga dalilin shikan, shi dai kawai shigowa yayi ya miƙa mata takaddar saki ya kuma ce yabata wunin yau kaɗai ta tattare kayan ta tabar gidan, a lokacin yayah auwalu yana tare da ita, shiru yayi yana sauraron kukan goggo wanda gaba ɗaya ta rame ta fita a hayyacinta, sai ɗan dogon hanci a fuskanta, fita yayi yaje ya gayawa inna, babu ɓata lokaci Inna ta turo ƙanwar ta inna ƴanbiyu, haka aka tattare kayan goggo aka dawo da shi ɗakinta na gidan Malam Garba, dama akwai sauran kayan ta a ciki har da katifan ta na da, dayake ɗakin ciki biyu ne da parlor a tsakiya, su yaya suna ɗayan ɗakin goggo ta dawo nata ɗakin,abun tausayi tunda goggo ta dawo lafiya ya gagara, laulayi na yau daban na gobe da ban, haka inna ƴanbiyu ta dawo ta zauna da ita, saboda inna tana fama da ciwon ƙafa sosai, cikin goggo na wata bakwai amma bata taɓa zuwa awon ciki ba, domin tun da ta fito Alƙali bai taɓa waiwayan ta ba, lokacin da yayan Baban mu ya tare shi da maganan zuwanta asibiti cewa yayi ba zai iya ba, cikin ma taje ya bar mata shi duniya da lahira, shi sauran yaran da yake da shi ma sun ishe shi rayuwar duniya.
Gidan Alhaji inuwa mai Gwal shine gidan da yake maƙwabtaka da mu ta gefen dama, gida ne da zance duk kobi babu gidan da aka tara ƴan gayu masu tafiya da zamani a gidan, Babban ɗan shi Garba inuwa ma'aikaci ne a banki, lokacin yana ji da tashen samartaka da kuɗi, domin ɗan gata ne a wajen mahaifin shi, don kuwa shi kaɗai ya haifa ɗa namiji kuma babba, sai ƙannen shi mata guda biyu, bai daɗe dayin aure ba yana xaune a fadaman mada, amma duk weeƙand yana gida da amaryar shi wacce ake ƙiranta Aunty Rashidah, ma'aikaciyar asibiti ce mai bala'in tsabta, gata da sauƙin kai da son mutane, gata ƴar masu kuɗi don lokacin idan akace miki gidan mutane a GRA ne tou shi na musamman ne, Goggo na ta iya kitso sosai, lokacin sai surkuwar ta matar Alhaji Inuwa mai suna Dadda tasaka ƙannen Garba suka rakota kitso wurin Goggo, shigowanta wurin goggo taji a zuciyarta Goggo ta mata domin yanayi tsabtar Goggo da haƙurin ta ya taɓa zuciyar Aunty Rashidah, shigowan ta na biyu ta samu Goggo tana jiƙa shinkafan masan ta na gobe, domin Goggo da taji sauƙi sai ta riƙe sana'ar Inna na suyan masa domin su rufawa kansu asiri, ita kuma goggo ƴanbiyu da yake bata taɓa haihuwa ba tana nan tare da su domin kula da inna.
Sun zauna yin kitso Aunty Rashida ta tambayi Goggo a wani asibiti take awo? Murmushi kawai Goggo tayi ta gyara ta fara tsaga kanta domin kitse mata shi, har suka gama yaryara kitson goggo bata ce mata komai game da maganan awon cikin ba, har sai da zata fita tacewa Goggo gobe idan anyi masan zata turo driver ya karɓa musu da yake sunday ne, sannan ta miƙawa goggo kuɗi mai ɗan kauri tace ta shiryah taje asibiti domin fara awo, cike murna goggo tayitq godiya, wanda har inna da inna ƴanbiyu suka fito suna tayata, idon inna cike da hawaye take duban goggo da take ta share hawayen da yaƙi tsaya mata a idon ta.
**********
Ai kuwa ranan monday goggo batayi aikin masa ba tabarwa su inna ta wucce asibiti, haka ma'aikatan sukayi ta mata masifan rashin zuwa da wuri, ita dai bakin ta shiru sai ido da take bin su da shi, bayan angama komai ta fito zata dawo gida suka haɗu da Aunty Rashida da ta fito gaisuwa cikin asibitin specialist ɗin, ganin goggo na ta sauri zata tari abun hawa domin tafiya ta tsayar da ita,
Goggo fuskanta ɗauke da murmushi ta tsaya suna gaisawa, murmushi daya kasance nida ƴan biyu mu muka ɗauke shi, domin ni ba sosai ake gane abun da yaɓata mun rai ba kamar Goggo na, don fudkan mu kullum ɗauke yake da mirmushi, wannan kuma ba wani abu bane na daban halittah ne da Allah ya kanyi mutum da shi, bawai rashin aji bane ko kamun kai, kawai halittah ne na ubangiji, ya faɗa yana duba na alokacin fuskan shi ɗauke da murmushin, nima murmushin nayi ina sunkuyar da kaina ƙasa, don samun kaina nayi da jin kunyan shi mai girman gaske *Aunty nice* ga shi murmushin shi wani irin kyau yake ƙara mishi, gaskiya *Aunty nice* M.G mai kyau ne, kyaun da idan kina kallon shi zakiji zuciyar ki tana samun nutsuwa na musamman, gashi M.G mutum ne mai zuciya mai kyau.
Murmushi nayi ina kallon fuskan hajiya ayshaa da take wani lumshe ido tana buɗewa cike da yanga, daga alama kuma zuciyar ta ba ƙaramin so takeyi wa M.G ba, domin sunan shi kawai idan ta ambata sai naga fara'a a kan fuskarta.
*AUNTY NICE*
managarciya