Ka san adadin gishirin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince ka ci kullum?

Ka san adadin gishirin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta amince ka ci kullum?

Cin gishiri a cikin abinci ko abinsha fiye da ƙima na iya kawo hawan jini. Sannan hawan jini na da haɗarin kawo cutukan zuciya da jijiyoyin jini.

Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma Gidauniyar Zuciya ta Birtaniya sun ƙayyade tare da amince yawan gishirin da ya kamata mutum ya ci a kullum cewa ya zamanto ƙasa da ma'aunin giram shida (<6g), wato kwatankwacin mitsitsin cokalin shayi guda kenan kawai.

Sai dai, an lura cewa kaso uku cikin huɗu(3/4) na yawan gishirin da ake ci ba a sanin an ci. Saboda ana zuba gishirin ne tun lokacin da ake sarrafa abinci ko abinsha. Saboda haka, abu ne mai matuƙar wahala ka iya gane yawan gishirin da ka ci a kullum. 

Abubuwan da ke maƙare da gishiri sun haɗa da: nau'o'in magi, musamman farin magi, burodi, biskit, kek, yagwat, lemukan gwangwani/roba, sarrafaffen abinci da ke zuwa a leda, gwangwani ko roba, da dai sauransu.

Domin ƙaurace wa cin gishiri fiye da ƙima, ana iya amfani da barkono ko sauran jinsinsa, kayan ƙamshi, ciyayi/ganyayyaki, tafarnuwa, albasa, ruwan lemon fata da sauransu domin samar da ɗanɗanon abinci maimakon amfani da tsurar gishiri ko magi.

Ƙayyade ko ƙaranta cin gishiri zuwa ƙasa da giram shida a kullum zai rage haɗarin kamuwa da:

- hawan jini

- bugun zuciya

- shanyewar ɓarin jiki

- kassarewar zuciya

- da sauran matsalolin zuciya da jijiyoyin jini.