Gwamna ya amince da gyara masallaci 100 a jihar Kebbi

Gwamna ya amince da gyara masallaci 100 a jihar Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Dakta Nasir Idris Kauran Gwandu ya amince da ginawa da sake gyaran masallatai 100 a fadin jihar.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin addini Injiniya Imrana Usman ya furta jim kadan bayan yana duba aikin wasu masallatai a cibiyar jihar waton Birnin Kebbi.
A cewarsa masallaci 40 da ake sallah biyar ta yini ne za a gyara a babban birnin, yayin da sauran 60 suna a kananan hukumomi,  kowace karamar hukuma za a dauki masallaci uku.
Mai baiwa gwamnan shawara ya ce aikin za a kammala shi a karshen wannan shekara, ya kuma bayyana gamsuwarsa yadda 'yan kwangilar ke tafiyr da aikin a dukkan masallatan jumu'a da ya ziyarta.
Ya bayyana gwamna ya amince da lissafin aikin da aka kaima masa ba tare da rage komai ba, "Kebbi ba ta taba samun lokacin da ake yi wa addini hidima kamar a wannan gwamnati ba."
Ya kuma bayar da tabbacin gwamnati ba za ta yarda da aiki marar inganci ba.