Maganin Karfin Maza: Kasuwannin Kano Sun Cika Da Magunguna

An bayyana cewar kasuwanni a jihar Kano suna nan cike makil da magungunan karin karfin maza. Hukumar dake sanya ido da kula da harkokin faskwauri ta kasa da kuma hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya ne suka bayyana haka a Kano.

A cewar hukumomin biyu, duk kasuwanni a Kano in ka zaga babu abinda aka fi talla kamar maganin karin karfin maza.

Hukumar ta kara da cewar galibin magungunan da ake talla ba su da lasisi, kuma masu illatarwa ne ga lafiya.

Hukumomin sun bayyana cewar karuwar laifukan ta'addanci da ake fama da su a jihar nada alaƙa da shaye shayen ƙwayoyin ƙarfin maza da ake yi wanda suke jirkita hankali da karin kuzarin da ya wuce kima.

Hukumomin sun bayyana cewar matasa na fama amfani da kwayoyin karin karfin maza wanda yake kara musu kuzari fiye da lissafi, abin da kan sanya su aikata miyagun laifuka da suka hada fa fyaɗe da kuma ta'addanci.

Wannan matsala ce jihohin Arewa ke fama da ita kusan kowace kasuwa za ka samu ana wannan kasuwancin.

Yakamata mutane su yi wa kansu karatun ta natsu kan tafiyar da sha'anin rayiwarsu don ba ta muhimmancin da yakamata.

~ Daily Nigerian Hausa: