Za a Riƙa Yi Wa Tambuwal Addu'ar Samun Aljanna Bayan Barinsa Ofis------Sarkin Musulmi

Za a Riƙa Yi Wa Tambuwal Addu'ar Samun Aljanna Bayan Barinsa Ofis------Sarkin Musulmi
Tambuwal da Sarkin Musulmi

Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya bayyana cewa ba za a manta da irin aiyukkan alherin da gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta aiwatar ba hakan zai sa a rika yi masa fatan alheri bayan barin mulkinsa.
Sarkin Musulmi a wurin bukin buda cibiyar gwaje-gwajen kiyon lafiya da gwamnatin jiha ta samar ne ya furta hakan ya ce Tambuwal zai bar ayyukan da za a riƙa tunawa da shi wannan cibiyar na ciki.

Ya ce Tambuwal bayan yabar ofis in sha Allah mutane za su cigaba da yi  masa addu'ar samun aljanna da sauran shugabanni.
Sa'ad ya ce akwai buƙatar samar da cibiya irin wannan domin taimakawa al'umma a haujin lafiya.
"mun godewa wannan hangen nesan, sai dai akwai buƙatar a samu yanda za a riƙe aikin nan da yanda talaka zai amfana da aikin, a ko'ina ka zo da kuɗi kaɗan za ka iya samun abin da kake buƙata," a cewarsa.
Cibiyar da aka gina a unguwar Farfaru ta laƙume kuɗi biliyan 3.2, an gina ta kan kuɗi miliyan 824, kayan aikin cibiya an sawo su kan biliyan 2.4, da suka ƙunshi gwaje-gwajen ciruta da ɗan adam.