‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wasu Ma’aurata Biyu A Abuja

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Wasu Ma’aurata Biyu A Abuja

Masu garkuwa da mutane sun dauke wasu ma’aurata, Mista Sunday Odoma Ojarum da Mai dakinsa, Janet Odoma Ojarume dake zaune a birnin Abuja.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa masu garkuwa da mutane sun yi awon-gaba da wadannan Bayin Allah a ranar Lahadin nan in da suka samu nasarar tafiya da su.</ p>

Abin ya faru ne a unguwar Sheda da ke cikin karamar hukumar Kwali a birnin tarayya Abuja. Wani mazaunin Sheda, Japhet Musa ya shaidawa Daily Trust cewa abin ya auku ne a safiyar ranar Lahadi, 24 ga watan Yuli, 2022.

Japhet Musa yake cewa ‘yan bindigan sun shigo unguwar ta su ne dauke da miyagun makamai. A cewar mazaunin, masu garkuwa da mutanen sun kafa kansu a wasu sanannun wurare, daga nan suka haura gidan ma’auratan.

Musa yace cikin tsakar daren miyagun suka lallaba cikin daren suka dauke Sunday Ojarum da matarsa, Madam Janet Ojarume.

A ranar Litinin kuma, matar mutumin ta tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun shiga gidan na su, ta ce ta katanga aka hauro masu ana barci.

 Kamar yadda ta ke fada, bayan sun dauke su, jagoran ‘yan bindigan ya bada umarni a kyale ta, ta koma gida domin karbo kudin fansa.

Matar ta ce a lokacin da aka shigo gidan, yaransu biyu su na kwance sai ba a taba su ba amma aka tafi da uwaye.

Har zuwa yanzu dai ‘yan bindigan ba su tuntubi iyalin ba kan nawa suke bukatar a ba su da in da za a kai masu kudin.