'Yan Najeriya Ba Su da Dalili  Na Zama Cikin Ƙangin Talauci----Tinubu

'Yan Najeriya Ba Su da Dalili  Na Zama Cikin Ƙangin Talauci----Tinubu

 

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, ya ce ‘yan Najeriya ba su da wani dalili na zama cikin talauci, Channels tv ta ruwaito. 

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnonin da aka zaɓa a inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Tinubu ya roƙi gwamnonin su tsara tare da aiwatar da manufofin masu kyau ga dukkan ‘yan Nijeriya kuma su duba maslahar kasa a koda yaushe sama da burikansu na siyasa. 
“Ba mu da dalilin zama matalauta. Idan muka duba inda muka fito, halin da muke ciki, dalilin da ya sa muke fama da ƙarancin ababen more rayuwa, da ilimi mara inganci, da karancin cibiyoyin kiwon lafiya, zamu ga ƙasar mu mai albarka ce." 
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar an haƙaito Tinubu na cewa Najeriya ba gurɓatacciyar ƙaa bace, tana da albarka da tarin ni'ima.