Masarautar Zuru Ta Nada Wasu Daga Cikin 'Ya'yanta Da Suka Yi Fice
Masarautar Zuru da ke a jihar Kebbi ta yi sabbin nade-naden sarautar gargajiya ga wasu daga cikin 'ya'yanta da suka yi fice.
Sarkin Zuru, Mai martaba Manjo Janar Muhammadu Sani Sami na biyu ne ya jagoranci yin nadin albarkacin cikansa shekaru 80 a duniya.
Daga cikin wadanda aka yi wa nadin har da tsohon karamin ministan Kimiyya da Fasaha Farfesa Muhammad Abubakar Ka'oje.
Bikin nadin wanda ya gudana a jiya Asabar, ya samu halartar masu rike da Sarautar Gargajiya na masarautar da Hakimai 'yan siyasa ciki har da Dan Majalisar mai wakiltar kananan hukumomin masarautar, Hon. Kabir Ibrahim Tukura (Gamjin Zuru).
Abbakar Aleeyu Anache
managarciya