Gwamna Buni Ya Sanyawa Kasuwar Nguru Sunan Shiekh Ngibirma
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya sanyawa sabuwar kasuwar da gwamnatinsa ta kammala ginawa a garin Nguru a jihar (Nguru International Modern Market), sunan Shehun Mallamin addinin musulunci a nahiyar Afrika: Shiek Muhammad Ngibirma.
A sanarwar manema labaru, mai dauke da sa-hannu Darakta-Janar kan hulda da yan jaridu da kafafen yada labarai a ofishin Gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed, da yammacin ranar Alhamis a lokacin da Gwamnan ya karbi bakoncin Mallama Aisha AbdulMutalib, yar asalin garin Potiskum, wadda da tayi nasarar zama zakaran gasar karatun Alkur'anin Mai Tsarki (rukunin mata) a garin Gusau ta jihar Zamfara.
Gwamna Buni ya bayyana jindadinsa dangane da kokarin Mallama Aisha, inda ya nunata a matsayin abin alfahari ga jihar Yobe.
Sakamakon haka, Gwamna Buni ya gwangwaje Hafiza Aisha da kyautar gida, kuma ya nadata a matsayin mai bashi shawara kan harkokin abubuwan da suka shafi haddar Alqura'ni Mai Tsarki, tallafin gurbin karatu da kujerar aikin Hajji tare da mijinta.
Har wala yau kuma, Gwamnan ya bai wa dukan yan kwamitin da suka jagoranci gasar karatun Alkur'anin zuwa samun wannan nasarar kyautar kujerun aikin Hajjin bana.
Alhaji Mamman Mohammed ya kara da cewa, Gwamna Buni ya jaddada ribanya kokarin gwamnatinsa wajen samar da ingantaccen ilimin addinin musulunci da na boko a jihar.
Gwamna Buni ya kara da cewa, kuma a matsayin jihar Yobe a cikin tsohuwar Daular Ngazargamo wadda aka santa da hidima tare da yada ilimin addinin musulunci, wannan zai ci gaba da kasancewa a zahiri wajen tanadar kyakkyawan sunan da aka san Daular dashi.
A hannu guda kuma, Gwamna Buni ya amince da sanyawa sabuwar kasuwar zamani, wadda gwamnatinsa ta kammala ginawa a garin Nguru: sunan Shehun Mallamin addinin musulunci a nahiyar Afrika- Shiek Ngibirma Modern Market.
Yayin da Gwamna Buni ya bayyana cewa ya yi hakan ne domin tunawa da marigayi, Shehun Mallamin, wanda ya bayar da gagarumar gudumawa wajen yada addinin musulunci a wannan nahiyar.
"Sannan kuma a matsayin sa na Mallamin Addinin musulunci a fadin duniya, wanda al'ummar musulmin duniya ke girmamawa, bisa gudumawar da ya bayar." In ji Buni.
managarciya