Da Wuya A Samu Wanda Zai Maye Gurbin Janar Wushishi---Gwamnan Neja

Da Wuya A Samu Wanda Zai Maye Gurbin Janar Wushishi---Gwamnan Neja
Daga Babangida Bisallah, Minna
Rashin marigayi Janar Muhammadu Inuwa Wushishi mai ritaya babban rashi ne da cike gurbinsa zai yi wuya. Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya bayyana hakan jin kadan da kammala jana'izar marigayin jiya  talata a masallacin Sultan Bello da ke garin kaduna.
Gwamnan yace, babu wasu kalmomin da za ka iya anfani da su wajen jajanta wannan babban rashin na marigayin, idan an yi dubi da irin qwarewarsa, da bada shawarwari masu anfani da kuma kwarin guiwarsa wajen shirya ayyukan cigaba a matsayinsa na dattijo.
" A matsayinsa na shugaban al'umma, tsayayyen mutum. Dole mu farka akan jin wannan babban rashin da muka samu labarinsa.
Rashi ne da yayi tasiri a zukatan mu da zai tsaya tsawon lokaci ba mu manta da shi ba, saboda ya samar da shugabanci na gari a matsayinsa na dattijo". A cewar gwamnan.
Gwamnan yace mamacin wanda tsohon shugaban rundunar soja ne a kasar nan, yayi rayuwar ganin komai ya tafi yadda ya dace.
Yayi addu'ar Allah ya gafarta mai kurakuransa, ya kuma saka ma shi da gidan aljanna, ya kuma baiwa iyalansa juriya na hakurin wannan rashin.
Manyan jami'an tsaro da suka yi ritaya da wadanda ke aiki na daga cikin wadanda suka halarci sallar, sun hada da tsohon shugaban kasa, Janar Abdussalam Abubakar, mai ritaya, Kanal Sani Bello mai ritaya tsohon gwamnan jihar Kano, sai mai martaba Etsu-Nupe, shugaban majalisar sarakunan Neja, Alhaji Yahaya Abubakar wanda tsohon janar din soja ne.
Sauran sun hada da ministan tsaro, Bashir Magashi, shugaban rundunar sojan kasa, Lutanal Janar Faruk Yahaya, da mai taimakawa shugaban kasa akan sadarwa, Malam Garba Shehu da wasu manyan jami'an gwamnati da suka samu wakilci.