Tinubu ya sauke shugaban NNPC, Mele Kyari tare da naɗa wani
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya cire shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, Mele Kyari tare da duk mambobi kwamitin gudanarwar kamfanin.
Kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a safiyar yau Laraba.
Ya baiyana cewa Tinubu ya sanar da Bashir Bayo Ojulari a matsayin wanda ya maye gurbin Kyari a matsayin shugaban NNPCL.
Haka zalika Tinubu ya naɗa sabbin mambobin kwamitin gudanarwar karkashin shugabancin Ojulari, in ji Onanuga.
managarciya