'Yan bindiga sun yi garkuwa da hakimin kauye a jihar Kaduna da wasu 14
Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da hakimin kauyen Ungwan Babangida, da wasu mutane 14 a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna a daren ranar Alhamis.
Shugaban matasan Dokan Karji, Aminu Khalid, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da City Round a ranar Juma’a.
A cewarsa, maharan sun kai farmaki kauyen Ungwan Babangida ne da tsakar dare tare da manyan muggan makamai suna harbe-harbe a wasu wurare kafin daga bisani su tafi da su.
Wannan lamarin ya faru ne sa’o’i 48 bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu manoma hudu a kauyen Libere ranar Laraba a karamar hukumar.
Daga Abbakar Aleeyu Anache
managarciya