Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin dubin watan Sha'aban

Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin dubin watan Sha'aban
 

 
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama'a da su fara duban watan Sha'aban wanda ake kira watan Shan Ruwan Azumin Tsoffi daga gobe Laraba  29 ga watan Rajab 1446  wanda ya yi daidai da 29 ga watan Junairun 2025.
Shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini a masarautar Sarkin musulmi, Wazirin Sakkwaato Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya rabawa manema labarai a jiha.
Wazirin Sakkwato ya ce duk wanda ya samu ganin jinjinrin watan Rajab ya sanar da Hakimi ko Uban kasar da ke kusa da shi anan ne za a kai maganar ga Sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar.
Ya roki Allah ya taimake su a cikin wannan aikin da suke yi na addini.