Jam'iyar PDP Ta Mutum Uku Ce In Baka Cikinsu Ka Fita----Lamido

Jam'iyar PDP Ta Mutum Uku Ce In Baka Cikinsu Ka Fita----Lamido

Dan takarar Sanata a yankin Sakkwato ta Gabas cikin jam'iyar APC Alhaji Ibrahim Lamido ya bayyana mutanen da ke jam'iyar PDP kashi uku ne duk wanda ke tafiyar ba sa wuce su don haka suke  a an karar da mutane in ba ka cikin tsarin ka barta yafi maka ko ka ci gaba da shan wahalar rayuwa, ka  zo a yi  tafiyar su da take ta gaskiya ce.

Ibrahim Lamido a karamar hukumar Gwadabawa lokacin da ya tafi karbar wadanda suka sauya sheka daga jam'iyar PDP zuwa APC kimanin mutum dubu goma da ashirin (10020) a Lahadin data gabata ya ce "jam'iyar PDP ta mutum uku ce da suka hada da masu son zuciya da wadan da ake tafiya  a makance makafi kenan da masu son kansu kadai, makafi 'yan biya yakamata a fadakar da su wannan tafiyar ba ta su ba ce su yi tunani su zo in da ake tafiyar gaskiya a APC", a cewar Lamido.
Alhaji Lamido ya sanar da mutanen yankin matukar ya samu nasara zai kara tashi tsaye sama ga abin da yake yi yanzu a samar da tsaro da saukin rayuwa a yankin Sakkwato ta gabas.
Ya ce a jam'iyar APC duk daya suke mutane ne masu son cigaban al'umma da jiha da kasa baki daya don haka yake bukatar mutane su mara masu baya a zabe su don tabbatar da nasarar mutanen  jiha a fannin ilmi da kasuwanci da sauran bukatun rayuwa na yau da kullum.