Shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattawa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana baƙincikinsa kan harin da aka kaiwa wasu matafiya 25 da ba su ji ba su gani ba, a ƙaramar hukumar Sabon Birni dake jihar Sakkwato.
>
A bayanin da Sanata ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa Hassan Sahabi Sanyinnawal a ranar Talata ya nuna jimaminsa kan mutuwar mutanen da suka yi yunƙurin tafiya wani ɓangaren ƙasa.
Ya miƙa gaisuwar ta'aziyar ga iyalan margayan ya ba da tabbacin jami'an tsaro za su cigaba da kokari har sai an kawar da batagarin daga cikin al'umma.
Wamakko ya yi kira ga mutane su cigaba da bayar da goyon baya ga kokarin gwamnatin tarayya na samar da tsaro.