Sanata Gobir Ya Tallafawa Iyalai 90 Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga Ya Shafa A Yankinsa 

Tallafin wanda Sanata Ibrahim ya bayar dai nada manufar tallafawa iyalan mutane 90 da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a kauyukkan Dundai, Tunbulla Rakaƙa, Tursa, Gawon Fulani, Cikalto, Dargo, Dalijan, Rara da sauran kauyukkan karamar hukumar mulkin ta Rabah. Sanatan wanda tsohon shugaban karamar hukumar ta Rabah kana shugaban kwamitin rabon tallafin Alhaji Ibrahim Raba ya wakilta, yace ko wane daga cikin iyalan wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa dasu zasu samu tallafin naira dubu N20,000 ko wannen su. “Munzo nan garin Mai Kujera ne bisa domin bayar da wannan tallafin da Sanata Ibrahim Gobir ya bayar ga mutanen wannan karamar hukumar, wani wadanda ibtila'i ya sama, abinda kunka sani ne ibtila'o'i da yawa sunyi ta faruwa a wannan karamar hukuma, to saboda wasu matsaloli na aiki wadanda basu bar wata kafa wadda shi Sardauna ya sami tahowa nan domin wa mutane jaje, amma duk da haka a ‘yan kwanukka nan  saboda ya ga abin ya yi d'an tsaiko to ya ware lokaci ya taso ya taho domin shiwa mutane jaje, a lokacin wannan jaje da yazo karamar hukuma daga nan ne ya bayar da wannan tallafin yacce a baiwa iyalan su mamata din na wa'yanda ibtila'o'in nan sunka fada ya bayar domin a rabawa mutun 90, sannan abinda kunka sani ne irin wannan tallafin anyi bayar dashi a lokuttan da sunka shige”

Sanata Gobir Ya Tallafawa Iyalai 90 Da Hare-Haren ‘Yan Bindiga Ya Shafa A Yankinsa 

Daga Aminu Amanawa, a Sakkwato.

Dan majalisar dattawa mai wakiltar kananan hukumomin gabashin Sokoto da matsalar tsaro ta addaba Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir, ya bayar da tallafin Naira miliyan daya da dubu dari takwas ga iyalan wadanda hare-haren"yan bindiga ya shafa a karamar hukumar mulkin Rabah.

Tallafin wanda Sanata Ibrahim ya bayar dai nada manufar tallafawa iyalan mutane 90 da hare-haren ‘yan bindiga ya shafa a kauyukkan Dundai, Tunbulla Rakaƙa, Tursa, Gawon Fulani, Cikalto, Dargo, Dalijan, Rara da sauran kauyukkan karamar hukumar mulkin ta Rabah.
Sanatan wanda tsohon shugaban karamar hukumar ta Rabah kana shugaban kwamitin rabon tallafin Alhaji Ibrahim Raba ya wakilta, yace ko wane daga cikin iyalan wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa dasu zasu samu tallafin naira dubu N20,000 ko wannen su.
“Munzo nan garin Mai Kujera ne bisa domin bayar da wannan tallafin da Sanata Ibrahim Gobir ya bayar ga mutanen wannan karamar hukumar, wani wadanda ibtila'i ya sama, abinda kunka sani ne ibtila'o'i da yawa sunyi ta faruwa a wannan karamar hukuma, to saboda wasu matsaloli na aiki wadanda basu bar wata kafa wadda shi Sardauna ya sami tahowa nan domin wa mutane jaje, amma duk da haka a ‘yan kwanukka nan  saboda ya ga abin ya yi d'an tsaiko to ya ware lokaci ya taso ya taho domin shiwa mutane jaje, a lokacin wannan jaje da yazo karamar hukuma daga nan ne ya bayar da wannan tallafin yacce a baiwa iyalan su mamata din na wa'yanda ibtila'o'in nan sunka fada ya bayar domin a rabawa mutun 90, sannan abinda kunka sani ne irin wannan tallafin anyi bayar dashi a lokuttan da sunka shige”
“Wadannen tallafin na iyalan mutanen da abin ya shafa daga baya bayan nan dan ka da a zaka ana rabon abinnan wasu su dauka cewa a'a ai su ba'a basu ba kuma sun rasa iyalan su,  a'a wannan na wadanda abin ya shafa ne inji shugaban kwamitin.
Suma wasu daga cikin wadanda suka amfana da tallafin sun godewa dan majalissar dattawan bisa tallafin da ya basu.
“Eh gaskiya naji dad'in hakan, Allah ya saka da alkhairi, kuma gaskiya an kula Ubangiji Allah ya saka da alkhairi, dafarko gaskiya munga laifin gaskiya ba'a kula damu ba kan irin abubuwan da suka faru damu, amma yanzu gaskiya hakan da a kayi gaskiya munga an kula damu munji dad'in hakan inji kane ga wani daga cikin wadanda matsalar ‘yan bindigar ta shafa.