Sarkin Musulmi Ya Aiyana  Alhamis ta zama 1 ga watan Zulhijja

Sarkin Musulmi Ya Aiyana  Alhamis ta zama 1 ga watan Zulhijja

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya aiyana Alhamis 30 ga watan Yuli ce 1 gawata Zulhijja, hakan ke nuna ranar Assabar mai zuwa 9 ga watan Juli za ta zama ranar Sallar Layya(Salla Babba) 10 ga Zulhijja kenan.

A sanarwar da Farfesa Sambo Wali Junaidu Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini ga masarauta ya sanyawa hannu ya ce Sarkin musulmi ya yi fatan samun nasara da taimakon Allah ga musulmai.

Ya yi kira gare su da su yi addu’ar zaman lafiya da daurewar cigaba a kasar Nijeriya, da taya musulmai murnar Sallah Babba.