Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar Da Shirin Aiwatar Da Hukucin Kisa Kan Masu Garkuwa Da Mutane

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Kaddamar Da Shirin Aiwatar Da Hukucin Kisa Kan Masu Garkuwa Da Mutane

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Akalla jihohi 10 a Najeriya ne suka sha alwashin fara aiwatar da hukuncin kisa da kuma daurin rai da rai a kan duk wanda aka samu da laifin yin garkuwa da mutane, matsalar dake kara ta'azzara a cikin kasar.

Wannan matakin na zuwa  ne a daidai lokacin da alummar kasar ke cigaba da bayyana damuwa dangane da yadda matsalar ke neman gagarar hukumomin tsaro ganin yadda take karuwa a kowaccce rana. 

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da sufeto janar na ‘yan sandan kasar Olukayode Egbetokun, ya jibge runduna ta musamman a sassan jahohin kasar domin tunkarar matsalar da sauran laifukan da batagari ke tafkawa a cikin kasa.

Yayin zantawa da jaridar Punch a Najeriyar, gwamnatocin jihar Kano da Benue da  Bayelsa da Enugu da  Anambra da kuma Nasarawa sun tabbatar da matsayinsu dangane da aiwatar da dokar kisa a kan duk wani mai garkuwa da ya shiga hannu.

Hukumomi a jihar Kwara da Ondo da kuma Osun sun sha alwashin tabbatar da doka ta yi halinta na hukunta duk wanda aka kama da laifin da zaman gidan kaso na tsawon rayuwarsa.