Shin dagaske ne Tambuwal ya fara kamun ƙafar komawa jam'iyyar APC?
Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal a wasu bayanai da ba a tabbatar ba an ce ya fara kamun kafa ga tsohon Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari domin komawa jam'iyyar APC saboda ganin su tare a wani hoto da aka ɗauka ƙasar waje in da wasu ke faɗin Ingila ne.
Wannan hasashe da wasu masu kama da shi ba su da gurbin zama a wannan yanayin.
Managarciya a nata bincike da wahalar gaske Tambuwal ya sake komawa APC kafin zaɓen 2023 kamar yadda wani na kusa da shi ya faɗi.
Ya ce ka yi tunanin Tambuwal ya shiga APC a wannan marar baka yi wa tunaninka adalci ba, domin yakamata ka yi wa kanka tambayar mi Tambuwal ya manta a APC wanda zai koma ya ɗauko, wane gidan siyasa ne da ba zai samu nasara ba sai da shi? Ka cire tunanin zai yi amai ya lashe.
Da ya juya kan maganar haɗuwarsa da Shehi a Ingila ya ce Tambuwal mutumin mutane ne a ko'ina za ka iya ganinsa da wanda ba su jam'iya ɗaya domin shi yana siyasa ba da gaba ba.
"Ko ka manta ya haɗu da Abdul'aziz Yari a Kano da Sakkwato kwanan baya, yanzu kuma don an gansu tare a shigo da maganar sauya sheƙa ba daidai ba ne hakan."a cewarsa.
Tambuwal a kwanan baya da gwamnan Zamfara ya koma APC an yi masa tambaya ko zai koma ya ce "Allah ya kiyaye" hakan ya sa a lokacin maganar sauya sheƙarsa ta mutu.
A duk wanda ya fahimci takun Tambuwal ba wani abu da ke gabansa saman takarar shugaban ƙasa, kuma jam'iyarsa ta PDP da yake shugaban gwamnonin PDP za ta fi masa sauƙin samun tikitin takarar bisa ya sake sabuwar sanwa.
In aka yi la'akari da ba wani Gwamna da ba ya son wanda ya ɗaga hannunsa ne zai gaje shi, Tambuwal yana da damar tsayar da wanda yake so a jam'iyarsa ba wanda zai ce masa a'a, saɓanin ya sauya sheka domin akwai wani jagora a APC da yake da ɗimbin magoya baya.
Waɗannan da wasu bayanai da ba a sanya anan ba sun nuna da wuyar gaske Tambuwal ya shiga jam'iyar APC, kan haka masu hasashen sauya sheƙarsa su dubi wani abu daban na siyasa.