Kotun Koli: Shari'ar Mainasara Da Shugaban APC A Sokoto Tsugunne Bai Kare Ba

Kotun Koli: Shari'ar Mainasara Da Shugaban APC A Sokoto Tsugunne Bai Kare Ba

Kotun kolin Nijeriya bayan zaman da ta yi a yau Litinin kan Shari'ar da aka sa gabanta da neman bukatar sauraren Karar da Mainasara Sani ya bukata.
Kotun Koli ba ta aminta da bukatar ba ganin yanda aka fita batun daukaka kara a baya sai yanzu aka dawo da maganar.
Lauyan da ke bibiyar Shari'ar a hirarsa da Managarciya ya ce maganar ba ta kare ba har yanzu in shi Mai Shari'ar yana da bukata zai yi sabon shiri ya daukaka kara zuwa ga Kotun Kolin Nijeriya, in ko baya bukata zai fita batun Karar daga wannan hukuncin(na yau).
A zaman, kotu bata rufe damar da ke akwai ga Mai Kara ba in yana da shawa zai  sake shiri ya sa Karar a gabanta domin duba korafin da yake son Kotun Koli ta duba.
Abin Jira a gani shawarar da Mai Karar zai yanke a nan  gaba.